?>

​Iraki:Rokoki Da Dama Sun Fada Cikin Sansanin Sojojin Sama Na Amurka A Kasar Iraki

​Iraki:Rokoki Da Dama Sun Fada Cikin Sansanin Sojojin Sama Na Amurka A Kasar Iraki

Akalla rokoki 6 ne suka fada kan sansanin sojojin sama na kasar Iraki dake Al-Balat mai tazarar kilomita 85 daga arewacin birnin Bagdaza, babban birnin kasar a jiya Litinin.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa rokoki uku ne a jere suka fara faduwa cikin sansanin da farko, sannan wasu uku sufa fada kusa da barikin.

Labarin ya kara da cewa babu wani rahoton dangane da wadanda suka jikata a wadannan hare-hare a har yanzu.

Sai dai har ya zuwa lokacin bada wannan labarin babu wata kungiya ko wani mutum wanda ya dauki alhakin kai hare-haren.

Wasu majiyoyin sun bayyana cewa rokoki 10 suka fada kan sansanin sojojin na Amurka sannan sun ce wasu sojojn Amurka da wasu ma’aikata irakawa a cikin sansanin sun ji rauni.

Wannan dai shi ne hare-hare na biyu kan sansanin sojojin na Amurka dake Al-Balad a cikin sa’o’ii 24 da su gabata. A ranar Lahadin da ya gabata ma an kaiwa wannan sansanin sojojin na ‘yan mamaya hare-hare.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*