?>

​Iraki:Dakarun Hashd Alshaabi Sun Hana Mayakan Daesh Shigowa Kasar Daga Syria

​Iraki:Dakarun Hashd Alshaabi Sun Hana Mayakan Daesh Shigowa Kasar Daga Syria

Dakarun gamayyar kungiyoyin sa kai masu tabbatar da tsaron kasar Iraki, wacce aka fi sani da Hashdushaabi sun sami nasara dakile wani kokarin na sulalewar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a garin Jurfun-Nasr daga arewacin lardin Babil.

ABNA24 : Majiyar dakarun ta kara da cewa a lokacin dawowansu daga aikin hana sulalenwar sai motarsu ta taka nakiya wacce mayakan na Daesh su ka dasa a kan hanya wanda kuma yayi sanadiyyar shahadar mutum guda.

Kafin haka dai dakarun Hashdu ne suke gadin dogayen sandunan wayoyin wutan lantarki a kasar wadanda kungiyar ta Daesh ta dade ta na lalata su. Kamar yadda ta yi a lardunan Diala da kuma Ninawa. A halin yanzu dai dakarun Hasdu su ne ginshikin tsaron kasar Iraki, sannan masu tallafawa sojojin da sauran Jami’an tsaron kasar ta Iraki.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*