?>

​Iraki: An Kai Hari Kan Wata Ayarin Motocin Sojojin Amurka A Lardin Kirkuk

​Iraki: An Kai Hari Kan Wata Ayarin Motocin Sojojin Amurka A Lardin Kirkuk

Labaran da suke fitowa daga kasar Iraki sun nuna cewa an kaiwa wata tawagar sojojin Amurka hari a yankin Kadisiyya na lardin Kirkuk daga arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya kara da cewa a jiya ma an kaiwa wata tawagar sojojin Amurkan hari a tsakanin yankin Yusufiyya da Mahmodiyya da ke arewacin birnin Bagadaza.

Kafin haka dai kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda a kasar ta Iraki sun sha alwashin sai sun kori sojojin Amurka daga kasar. Kuma sun kara da cewa zasu ci gaba da kai mata hare-hare har zuwa lokacinda zata kawo karshen samuwar sojojinta a kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*