?>

​Imam Khamenei: Matasa Suna Da Gagarumar Gudunmawa Da Za Su Bayar Wajen Gina Al’umma

​Imam Khamenei: Matasa Suna Da Gagarumar Gudunmawa Da Za Su Bayar Wajen Gina Al’umma

Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya aike da sako ga taron kungiyoyin dalibai musulmi a jami’ion kasashen turai karo na 55.

ABNA24 : A cikin sakon nasa wanda ya aike zuwa ga zaman taron kungiyoyin dalibai musulmi a jami’ion kasashen turai karo na 55, Imam Khamenei ya jadadda muhimmancin irin gudunmawar da matasa musamman dalibai da suka yi karatu a fagagen ilimomi daban-daban suke bayarwa domin ci gaban al’umma da kuma gina ta.

Ya ce abin da ya faru a wannan lokaci kimanin shekara guda ya zuwa na bullar cutar corona da kuam watsuwarta a duniya, ya nuna yadda matasa masu himma suka bayar da gudunmawa suke ci gaba da bayarwa a bangarori daban-daban na kiwon lafiya.

Jagoran ya ce, matasa masu karatu a bangarori na ilimi a jami’oi daban-daban, wannan babbar dama ce a gare su, wadda ya kamata su yi amfani da ita domin samun duk wani ilimi da zai ba su damar taimakon al’umma da kuma ci gabanta a dukkanin bangarori.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni