?>

​Hizbullah Ta Fitar Da Hotunan Muhimman Wurare Na Sojin Isra’ila Da Aka Dauka Daga Sama

A cikin wani faifan bidiyo da kungiyar Hizbullah ta fitar, ta nuna hotunan muhimman wurare na sojin Isra’ila da suke cikin birane, da suka hada da manyan barikoki na soji.


ABNA24 : Tashar Almayadeen ta kasar Lebanon bayar da rahoton cewa, faifan bidiyon wanda ita ce tashar farko da ta watsa shi a jiya Laraba, ya nuna yadda kungiyar ta Hizbullah ta bayar da cikakken bayani ta hanyar hotuna kan muhimman wurare na sojin Isra’ila wadanda aka dauka daga sama.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan jawabin da babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya gabatar ne, inda yake gargadin Isra’ila da cewa, idan ta yi shiga wani sabon yaki da kasar Lebanon, a wannan karon za ta fusaknci martani mafi tsanani, wanda ba ta taba gani ba tun daga lokacin da aka samar da ita.

A cikin wani bayaninsa a lokutan baya, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, suna da masaniya a kan dukkanin muhimman wurare na tsaro da na gwamnatin Isra’ila, kuma a duk lokacin da Isra’ila ta bude yaki da Lebanon, Hizbullah za ta kai hare-hare da wasu makamai na musamman a kan wadannan muhimamn wurare na Isra’ila tare da ragargaza su.

Manyan janar-janar na rundunar sojin Isra’ila dai sun sha nanata cewa, a halin yanzu Isra’ila ba a shirye take ta shiga wani sabon yaki tare da kungiyar Hizbullah ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni