?>

​Hasashen Bankin Duniya: Tattalin Arzikin Najeriya Zai Habaka Da Kashi 2.5 A 2022

​Hasashen Bankin Duniya: Tattalin Arzikin Najeriya Zai Habaka Da Kashi 2.5 A 2022

Bankin Duniya ya yi hasashen samun habakar tattalin arzikin Najeriya da akalla kashi 2.5 cikin dari a shekarar 2022, fiye da hasashen kashi 2.4 da bankin ya yi a 2021.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Alkaluman da bankin ya fitar kan hasashen tattalin arzikin kasashe ya ce tattalin arzikin Najeriyar zai rika habaka shekara bayan shekara wanda ke da nasaba da tashin farashin man fetur da kuma kudaden da kasar ke samu a bangaren sadarwa da hukumomin kudi.

Najeriyar mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika wadda kuma ta dogara da man fetur wajen samun kudaden shiga, alkaluman da Bankin na Duniya ya fitar ysun nuna cewa bayan samun karuwar tattalin arziki da kashi 2.5 a 2022 zai sake karuwa da kashi 2.8 a 2023.

Wasu daga cikin dalilan da za su taimakawa tattalin arzikin na Najeriya a cewar bankin akwai matakin kungiyar OPEC na rage yawan man da manyan kasashe masu arzikin man fetur ke fitarwa, da kuma wasu sabbin tsare-tsare da za su taimakawa kanan kasashe na kungiyar.

Sai dai duk da habakar tattalin arzikin kamar yadda bayanan bankin suka nuna, Najeriyar za ta ci gaba da fuskantar matsalolin da annobar covid-19 ta haddasawa bangaren samar da ayyukan yi, haka nan za a dauki lokaci kafin farashin kayaki ya daidaita musamman na abinci.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*