?>

​Hajji: A Yau Ne Mahajjata Suke Gudanar Da Tsayuwar Arafat

​Hajji: A Yau Ne Mahajjata Suke Gudanar Da Tsayuwar Arafat

A yau ne dai mahajjata suke gudanar da tsawuyar Arafat, bayan sun isa Mina tun jiya a ranar Tarwiyah, inda a yau Litinin kuma za su yi tsayuwar arafat har zuwa faduwar rana, wanda shi ne babban rukuni a cikin aikin hajji.

ABNA24 : Mina dai tana tsakanin Makka da Muzdalifah ne, kuma tana da tazarar kilo mita bakwai daga arewa maso gabashin haramin Makka mai alfarma.

Yana cikin mustahabban aikin hajji mahajjata su nufi Mina a ranar 8 ga watan zilhijjah kafin gushewar rana inda za su kwana a can a ranar Tarwiya domin shirin Arafa a ranar tara ga wata.

Wannan dai ita ce shekara ta biyu a jere da ake gudanar da aikin hajji a cikin yanayi na corona, inda hukumomin Saudiyya suka kayyade cewa mutane dubu sattin ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana saboda kaucewa yaduwar cutar corona.

Baya ga haka kuma dole ne mahajjatan su cika sharuddan da aka gindaya musu na yin allurar rigakafin cutar corona, da kuma kasancewa a cikin kasar ta Saudiyya a lokacin fara rijistar daukar maniyyaya.

Sannan kuma wajibi ne a kan mahajjatan su zama masu kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya da hukumomin kiwon laiya na kasar Saudiyya suka shata a yayin gudanar da aikin haji, da hakan ya hada da saka takunkumin rufe baki da hanci, da kuma bayar da tazara ta akalla mita biyu, da kuma wanke hannuwa da sanadarai masu kashe kwayoyin cuta.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*