?>

​Habasha Ta Bada Sanarwan Kawo Karshen Cika Madatsar Ruwa Ta Renaissance

​Habasha Ta Bada Sanarwan Kawo Karshen Cika Madatsar Ruwa Ta Renaissance

Kafafen yada labarai na kasar Habasha sun bada labarin cewa an kawo karshen aikin cika madatsar ruwan ta Renaissance karo na biyu a yau Litinin.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta a kasar Lebanon ta bayyana cewa a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne gwamnatin kasar ta Habsha ta shaidawa kasashen Sudan da Masar kan cewa ta fara aikin cika madatsar ruwan karo na biyu. Sanarwan dai ta sanya kasashen biyu suka garzaya zuwa kwamitin tsaro na MDD don tattauna batun da manya-manyan kasashen duniya. Sai dai taron nasu da kwamitin tsaron har yanzun bai fitar da wani bayani ba.

Har’ila yau kasashen biyu suna ganin kasar Habasha ta keta wata yarjejeniya tsakanin kasashen 3 wacce suka rattabawa hannu a shekara ta 2015 dangane da madatsar ruwan ta Renaissance.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*