?>

​Guterres Ya Bukaci A Yaki Ta’addanci A Najeriya Tun Daga Tushe

​Guterres Ya Bukaci A Yaki Ta’addanci A Najeriya Tun Daga Tushe

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna muhimmancin komawa zuwa ga tushe wajen yakar ta’addancin da ke addabar Najeriya yau.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Antonio Guterres ya yi wannan bayani nea lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen menama labarai a fadar Aso Villa da ke birnin Abuja.

Guterres ya yi zama da shugaba Muhammadu Buhari, bayan nan kuma ya hadu da ‘yan jarida. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi bayanin kokarin da ya ce suna yi wajen taimakawa gwamnatocin Afrika wajen murkushe masu tayar da zaune tsaye.

Ya ce: Idan ka yaki ta’addanci da karfin bindiga ne zalla, ‘yan ta’adda za su dawo su yake ka. “Amma idan aka yaki ‘yan ta’adda da karfin bindiga da kuma bibiyar tushen ta’addancin, ba za su samu damar ci gaba ba.

Daga cikin tsare-tsaren da za su kawo zaman lafiya a cewarsa, akwai karbar tsofaffin ‘yan ta’addan da suka ajiye makamai, a sama masu sabuwar rayuwa.

Guterres ya ce dole ne a tabbatarwa wadanda rikicin ta’addanci ya rutsa da su, an sama musu makoma.

Zuwan Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya taimaka masa wajen sanin mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira da sauran mutane ke ciki a kasar a cewarsa.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*