?>

​Dan Majalisar Holland Mai Kin Musulunci Ya Sake Maimaita Kalaman Batunci Kan Musulmi

​Dan Majalisar Holland Mai Kin Musulunci Ya Sake Maimaita Kalaman Batunci Kan Musulmi

Dan majalisar dokokin kasar Holland mai tsananin kiyayya da addinin musulunci Geert Wilders ya sake maimata kalaman batunci a kan musulunci

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A cikin wani bayaninsa da ya gabatar bayan kai harin filin jirgin sama na Kabul a kasar Afghanistan, dan majalisar dokokin kasar Holland mai tsananin kin jinin musulunci ya sake nanata irin kalamansa na batunci a kan addinin musulunci da musulmi.

A cikin kalamansa ya kirayi gwamnatin Holland da ta dauki matakin rufe iyakokin kasar domin hana musulmin Afghanistan kwararowa cikin kasar, inda ya kira musulmi da dukkanin mabiya manzon Allah (SAW) da kalmar dabbobi.

Ya ce Daesh ta sake bayyana a kasar Afghanistan, nan gaba kadan za ta shigo kasashen turai domin aikin ta'addanci, inda yake kokarin nuna aikin ta'addanci da cewa hakan koyarwa ce ta addinin muslunci.

Kungiyoyi da cibiyoyin musulmi a kasar Holland da kasashen turai da daba sun nuan rashin amincewarsu da kalaman na Geert Wilders, tare da bayyana hakan a matsayin abin da yake kara haifar da fitina a tsakanin mutane.

Tun a shekarun baya Wilders ya yi ta yin kalamai na batunci ga manzon Allah (SAW) da kur'ani mai tsarki, tare da tunzura magoya bayansa masu irin ra'ayinsa yin ayyuka na cin zarafin musulmi.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*