?>

​Bloomberg: Afirka Na Gab Da Fuskantar Hauhawar Farashin Abinci

​Bloomberg: Afirka Na Gab Da Fuskantar Hauhawar Farashin Abinci

Wani rahoto da cibiyar tattalin arzikin Afirka ta Kudu ta fitar ya bayyana cewa, hauhawar farashin kayan abinci a duniya zai haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Cibiyar ta bayar da rahoton cewa hakan na iya haifar da tashin hankali a cikin wasu al'ummomin idan gwamnatoci suka gaza rage tasirin matsalar.

A daya bangaren kuma kuma kamfanin dillancin labarai na "Bloomberg" ya nakalto wani bayanin bincike na masana tattalin arziki na gidauniyar Jack Neil da Petro van Eyck cewa,kayan abinci na da daga cikin abubuwa da suka fi tsada a mafi yawan kasashen Afirka, idan aka kwatanta da kasashe masu karfin tattalin arziki, saboda yanayin samayyar jama’a.

Rikicin Ukraine ya illa matuka wajen hana fitar da abinci, katse hanyoyin samar da kayayyaki, da fari da ya kawo cikas a bangaren noman alkama, wanda duka waddan nan abubuwa ne da suka sanya farashin ya yi tashin gwauron zabi.

Masu binciken sun ce hauhawar farashin kayan abinci, karin kudin man fetur da kuma karuwar rashin aikin yi na haifar da rudani a siyasance a nahiyar Afirka, lamarin da ya sa gwamnatoci ke mayar da hankali a cikin kasafin kudi wajen samar da wani abin da zai iya rage wa jama’a radadin wadannan matsaloli, duk da cewa gwamnatocin wasu kasashen da ba su samun wani gagarumin tallafi, suna iya fuskantar koma baya da kuma shiga matsaloli tsakaninsu da al’ummomin kasashensu.

Hukumar ta yi nuni da cewa, a kasashe masu ci gaban tattalin arziki, abinci ya kai kashi 15% na kwandon, yayin da a Afrika ya zarce kashi 25%, yayin da yake ci gaba da karuwa a wasu kasashe, ciki har da Habasha, da Zambia, da Sudan da kuma Najeriya, inda farashin kayan abinci ya karu har zuwa kashi 50%.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa, alkaluman farashin abinci na hukumar FAO ya karu da kashi 13 cikin dari, wanda shi ne mafi sauri da aka taba samu a cikin shekarun baya-bayan nan, kafin ya fadi kadan a watan Afrilun da ya gabata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*