?>

​Babban Hafsan Sojin Birtaniya Ya Ce Akwai Yiwuwar Barkewar Yakin Duniya Na Uku

​Babban Hafsan Sojin Birtaniya Ya Ce Akwai Yiwuwar Barkewar Yakin Duniya Na Uku

Babban hafsan sojin kasar Birtaniya ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar bullar yakin duniya na uku matukar sojojin kasar da kawayensu na Turai suka tunkari kasar Rasha a yakin da ta kaddamar kan kasar Ukraine.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Furucin sabon babban hafsan rundunar sojin kasar Birtaniya Patrick Sanders da aka nada kwanan nan ya janyo cece-kuce a lokacin da ya yi kira ga dukkanin sojojin kasarsa da su kasance cikin shiri da fatan samun nasara a duk wani yaki da za su yi a nan gaba.

Janar Patrick ya kara da cewa: Duk wani matakin kalubalantar kasar Rasha a yakin da ta daura kan kasar Ukraine yana nufin bullar yakin duniya ne na uku a duniya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*