?>

​Antonov: Akwai Hadarin Yiwuwar Barkewar Yaki Tsakanin Rasha Da Amurka

​Antonov: Akwai Hadarin Yiwuwar Barkewar Yaki Tsakanin Rasha Da Amurka

Jakadan kasar Rasha a birnin Washington Anatoly Antonov, ya bayyana cewa mika makamai ga kasar Ukraine wata hanya ce ta yin fito na fito tsakanin Rasha da Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wata makala da jaridar Newsweek ta buga, jakadan ya kara da cewa, "A bayyane yake cewa Amurkawa ba su da hangen nesa a cikin halin da ake ciki a yanzu.

Mahukuntan kasashen yamma wadanda suka hankoronsu shi ne yin galaba a kan Rasha, wannan hankoro nasu yana tattare da hadarin gaske, domin kuwa wannan ita ce hanyar da za ta kai su ga yin arangama ta soja kai tsaye tsakanin manyan kasashen biyu mafi girma na nukiliyaa duniya wato Rasha da Amurka, lamarin da ba zai yi wa duniya kyau ba.

Jakadan ya jaddada cewa shirin Amurka na "murkushe Rasha da takunkumi" ba shi da amfani kuma ba zai yi nasara ba, jakadan ya ce, "Ko shakka babu sanya takunkumin da ba a yi tunani ba yana kara dagula al'amura a tattalin arzikin Amurkan ne ita kanta.

Jakadan ya jaddada cewa, yunkurin na Amurka, "ko kadan ba zai shafi kudurin sojojin Rasha na cika ayyukan da aka sanya a lokacin aikin soji na musamman na kare al'ummar Donbass" da kuma kawar da sojojin kasar Ukraine daga yankin ba.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*