?>

​Ana Kai Ruwa Rana Tsakanin Faransa Da Amurka Da Kuma Australia

​Ana Kai Ruwa Rana Tsakanin Faransa Da Amurka Da Kuma Australia

Faransa ta kirayi jakadunta daga Amurka da Australia sakamakon abin ta kira cin amanarta daga kasashe aminanta, bayan da Australia ta sake kulla sabuwar yarjejeniyar cinikin jiragen yakin karkashin teku da Amurka da Burtaniya, wanda ya kawo karshen wanda ta fara kullawa da Faransa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa a yammacin Jumma’a ministan cikin gidan Faransa Jean Yves Le Drian yace Shugaba Emmanuel Macron ne ya bukaci daukar matakin saboda “girman sanarwar da Australia da Amurka suka yi a ranar 15 ga watan Satumba dake warware cinikin na Faransa da ya kai dala biliyan 40.

Rikicin diflomasiyyar da ba kasafai ake samu ba ga kawayen Faransa ya zo ne kwanaki biyu bayan da Australia ta sanar da soke wani cinikin sayan manyan jiragen ruwa na Faransa tare da maye gurbin cinikin da na jiragen ruwan Amurka masu amfani da makamashin nukiliya.

Tun a shekarar 2016 Austiraliya ta zaɓi wani kamfani mallakar gwamnatin Faransa da zai kera mata jiragen karkashin ruwa guda 12, kafin ta juya akalar cinikin zuwa Amurka.

Fadar White House ta bayyana kaduwarta kan matakin Faransa na kiran jakadanta gida, tana mai cewa Amurka za ta yi dukm mai yiwuwa wajen warware takaddamar kan batun cikinikin samarwa Australia jiragen yakin karkashin teku.

Wani babban jami’a a Fadar White House da ya bukaci sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP kan nadamar da suka yi, inda yace za su ci gaba da yin aiki a cikin kwanaki masu zuwa don warware bambance -bambancen da ke tsakaninsu, kamar yadda suka yi a wasu bangaorin kwancensu na twason lokaci a baya.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*