?>

​Amurka Ba Za Ta Tattauna Da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman Ba

​Amurka Ba Za Ta Tattauna Da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman Ba

Gwamnatin Amurka ta ce za ta tattaunawa da Saudiyya, amma da sarkin kasar Salman Bin Abdulaziz kawai, ba da yarima Muhammad Bin Salman ba.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da take zantawa da manema labarai a yammacin jiya, mai magana da yawun fadar White House a kasar Amurka Jane Psaki, ta bayyana cewa a halin yanzu babu wani shiri na tattaunawa da Saudiyya.

Ta ce idan har shugaba Joe Biden zai yi wata tattaunawa da Saudiyya, to zai tuntubi sarkin kasar ne Salman Bin Abdulaziz, ba dansa yarima Muhammad Bin Salman ba.

Ta ci gaba da cewa, ko shakka babu akwai canje-canje a cikin siyasar sabuwar gwamnatin Amurka dangane da kasar Saudiyya, amma duk da haka bangarorin biyu za su ci gaba da yin aiki tare a wasu bangarori, musamman ma taimaka Saudiyya ta fuskar kariya.

A kwanakin baya an tambayi Jane Psaki kan ko Joe Biden na niyyar kakaba wa gwamnatin Saudiyya takunkumi kan kisan Jamal Khashoggi, amma ta ki amsa wannan tambaya.

Gwamnatocin kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa UAE dai sun mara baya ido rufe ga tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a lokacin yakin neman zabe, da nufin ganin ya samu nasarar kayar da Joe Biden a zaben, wanda hakan hakan ya sanya gwiwar mahukuntan wadannan kasashe ta yi sanyi dangane da makomar alakarsu da Amurka, bayan da Trump ya sha kayi a zaben.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni