?>

​Amurka: Ana Karancin Gadajen Kwana A Asbitocin Kasar Saboda Yawan Marasa Lafiya Na Cutar Covid 19

​Amurka: Ana Karancin Gadajen Kwana A Asbitocin Kasar Saboda Yawan Marasa Lafiya Na Cutar Covid 19

A dai dai lokacinda cutar Covid 19 take kara yaduwa a cikin Amurka, an fara samun karancin gadajen kwana na wadanda basa da lafiya a Jihar Ohayo na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya bayyana cewa jaridun Amurka sun cika da sanarwa daga jami’an kiwon lafiyar kasar kan cewa duk wanda bai yi allura ba to suna rokonsa ya je yayi da gaggawa. Don su ne suke shan wahala idan wani yayi rashin lafiya.

A halin yanzun dai Amurkawa kimani miliyon 39 basu yi alluran riga kafin cutar ko na farko ba. Kuma mafi yawan masu kamuwa da cutar daga cikin wadanda suka ki yin alluran riga kafin ne. Bincike ya tabbatar da cewa mafi yawan wadanda suka ki yin alluran riga kafin cutar matasa ne farare fata.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*