?>

​Amurka: An Samu Gawar Diyar Malcolm X A Gidanta A Birnin New York

​Amurka: An Samu Gawar Diyar Malcolm X A Gidanta A Birnin New York

An samu gawar daya daga cikin 'ya'yan Malcolm X, shugaban musulmi bakaken fata a Amurka a cikin gidanta da ke birnin New York.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar New York Post ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, wata diyarta ce ta gano gawar Maliikah Shabbaz 'yar Malcolm X mai shekaru 56 a gidanta da ke Brooklyn New York, da misalin karfe 4:40 na safiyar ranar Litinin.Mutuwarta na zuwa ne a daidai lokacin da ake batun yiwuwar yanke hukunci kan mutanen biyu da ake zargi da kisan Malcolm X.A cewar kafofin yada labarai, masu bincike dai ya zuwa yanzu ba su zargin wani da aikata laifin kisanta, amma sun ce binciken da ake yi yanzu kan gawarta zai tabbatar da musabbabin mutuwarta.

Bernice King, diyar Martin Luther King Jr. (shugaban masu fafutukar kare hakkokin bakaken fata a Amurka, ta wallafa a shafinta na twitter cewa, tana nuna alhininta game da mutuwar Malikah Shabbaz, tana mai cewa: "Na yi matukar bakin ciki da rasuwarta.

Malcolm X shi ne shugaban musulmi bakar fata a kasar Amurka kuma musulmi mai rajin kare hakkin bil'adama, wanda ya yi gwagwarmaya domin kawo karshen zaluncin da ake yi bakaken fata a Amurka.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*