?>

​Amerika: Trump Ya Kashe Shahid Kasim Sulaimani Ne Don A Sake Zabensa

​Amerika: Trump Ya Kashe Shahid Kasim Sulaimani Ne Don A Sake Zabensa

Tsohon sakatarin harkokin tsaron kasar Amurka Mark Esper, a cikin wani littafin da ya rubuta dangane da ayyukansa a matsayin sakataren harkokin tsaron Amurka mai suna “A Sacred Oath “ ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kashe Shaheed Kasim Sulaimani ne don a sake zabensa a kan kujerar shugabancin kasar a zaben da ke gabansa a lokacin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tsohon sakatarin tsaron ya kara da cewa mai bawa tsohon shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro a lokacin ne Mr Robert O’Brien ya fada masa kan cewa shugaba Trump yana son kashe wani babban kwamandan dakarun juyin juya halin musulunci na Iran (IRGC) wanda ake kira Janar Qasim Sulaimani, wanda kuma yake gudanar da ayyukansa na yaki ta’addanci a wajen kasar Iran.

Esper ya kara da cewa ‘wannan aikin yana da matukar hatsari, kuma yana iya gamuwa da maida martani mai tsanani a bangaren kasar Iran. Don haka shi baya goyon bayan hakan.

Trump ya bada umurnin kissan Shahid Sulaimani da abokan tafiyar sa ne a ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta 2020 don yana son Amurkawa su sake zabensa kan kujerar shugabancin kasar, amma ya kasa cin zaben.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*