?>

​Akalla Mutane 17 Suka Bace Sanadiyyar Nutsewar Wani Jirgin Ruwan Daukar Kaya A Kasar Liberia

​Akalla Mutane 17 Suka Bace Sanadiyyar Nutsewar Wani Jirgin Ruwan Daukar Kaya A Kasar Liberia

Mutane akalla 17 suka bace bayan da wani jirgin ruwan daukar kaya mai suna Niko Ivanka ya nutse kusa da birnin Monrovia babban birnin kasar Liberia.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kafin haka ya faru, an hana jirgin motsawa daga tashar jiragen ruwa na Monrovia don rashin cika sharudda shiga ruwa.

Amma a ranar Asabar da ta gabata jirgin ya kama hanya zuwa wata tashar jiragen ruwa a kasashen kudancin Afirka.

Amma ba’a dade ba jirgin ya aika da sako shiga hatsari ga masu gadin jiragen ruwa a Monronia. Sannan kafin ma’aikatan ceto su isa inda jingin yake ya fara nutsewa.

Labarin ya kara da cewa an ceci mutane 11 daga halaka, amma wadanda suka tsiri sun bayyana cewa yawansu ya kusan 28, wanda ya nuna cewa kimani mutane 17 sun bace.

Hukumokin kasar Liberian sun ce an kama mai jirgin wani dan kasar China wanda yake cikin kasar a lokacinda hatsarin ya auku don karin bincike.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*