?>

​ Shugabanin Gabashin Afrika Na Taro Kan Rikicin DRC Da Rwanda

​ Shugabanin Gabashin Afrika Na Taro Kan Rikicin DRC Da Rwanda

Shugabannin kasashen gabashin Afrika na wani taro yau Litinin, don tattauna batun rikicin dake tsakanin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da makobciyarta Rwanda.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Taron shugabannin kasashen na gabashin Afrika 7 na zuwa a daidai lokacin dangantaka tsakanin Kigali da Kinshasa ke kara tsami game da batun ‘yan tawayen M23 da Jamhuriyar Congo ke zargin Rwanda da goyan baya.

A halin da ake ciki dai bangarori na ci gaba da kira ga kasashen biyu dasu kai zuciya nesa, don kaucewa wanzuyar rikicin a yankin.

Kasashen Uganda da Kenya, duk sun yi kiran a kai zuciya nesa domin kare rayukan fararen hula.

Kafin hakan shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, wanda ya bayyana damuwarsa game da halin da ake ciki, ya gana a jiya Lahadi da manyan kwamandojin soji na kasashen gabashin Afrika, ciki har da DRC, domin tattauna batun, a wani mataki na share fagen tattaunawa da shugabanin kasashen yankin.

Alaka tsakanin DRC da Ruwanda na kara tsami, inda a tsakiyar wannan mako mai karewa gwamnatin Kinshasa ta sanar da yanke duk wasu yarjeniyoyi dake tsakaninta da Kigali, tare da rufe iyakarta da kasar.

342/


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*