Boko Haram Ta Hallak Mutane Akalla Hudu A Jihar Bornon Nigeriya

Boko Haram Ta Hallak Mutane Akalla Hudu  A  Jihar Bornon Nigeriya

'Yan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani mummunan harin wuce gona da iri kan garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya, inda suka kashe mutane akalla hudu.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Samantha Newport ya bayyana cewa: Da almurun jiya Alhamis da misalin karfe 7 zuwa 8 wasu gungun mayakan kungiyar Boko Haram sun farma garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin Nigeriya, inda suka tarwatsa al'ummar garin da jami'an bada agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya.

Majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da kashe ma'aikatan bada agajinta guda hudu tare da jikkata guda, kuma daya daga cikin ma'aikatan ya bace babu labarinsa.

Shaidun ganin ido sun cewa akwai yiyuwar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon yadda mayakan kungiyar ta Boko Haram suka bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma harin ya tarwatsa al'ummar garin, inda ake tsammanin mutane fiye da 55,000 ne suka tsare daga muhallinsu


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky