?>

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi muzahara a Abuja domin tunawa da shahidan Quds na 2014

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi muzahara a Abuja domin tunawa da shahidan Quds na 2014

A yau laraba 26 ga watan Yuli 2017 ne daruruwan almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky suka yi gaggarumar muzahara a birnin tarayya Abuja domin tunawa da 'yan uwansu da aka kashe a lokacin muzaharan Quds ta 2014.
Sun fara muzaharan daga Area 2,suna tafiya cikin tsari da natsuwa suna dauke da hotunan Sheikh Zakzaky da banonin da aka rubuta free Zakzaky,Free Palastine.Suna rera waqoqi iri-iri wadanda suke alamta neman a yantar da Falasdinu,da kuma gwamnatin Nigeriya ta gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da mai dakinsa ba tare da sharadi ba.
Sun karkare muzaharan da kona tutan Isra'ila a park na Area 1,sannan suka yi addu'a kowa ya watse ba tare da wani abu ya faru ba kaman yanda majiyar mu ta shaida mana.
In ba a manta ba a shekarar 2014 ne a lokacin da almajiran Sheikh Zakzaky suka fito Muzaharan Quds a Juma'ar karshen Ramadan din shekaran ne, sojoji suka zo suka bude wuta akan masu muzaharan wanda yayi sanadin shahadan sama da mutum 30 wanda ya hada 'ya'yan jagoran harkar musulunci a Nigeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*