Iran Ba Ta Bukatar Shiga Wani Sabon Rikici Da Amurka_Ravanchi
Jakadan Iran, a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa Iran, ba ta bukatar shiga wani sabon rikici da Amurka.
Jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Iran ya bayyana cewa, kasashen turai ba su da gaskiya a tattaunawarsu da Iran kan shirinta na nukiliya.
Majiyar ma’aikatar tsaron kasar Yemen ta bada sanarwan cewa ta kai hare-haren maida martani a cikin kasar Saudiyya, tare da amfani da makamai masu linzami da kuma jirage wadanda ake sarrafasu daga nesa.
Babban jami’in ‘yan sanda na birnin Tehran, Husain Rahimi ne ya sanar da cewa, ‘yan sandan sun dakile wani shirin kai harin kunar bakin wake tare da kame dan ta’addar gabanin ya shigo cikin birnin Tehran.
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kasancewa a cikin yarjejeniyar nukiliya, matukar dai Amurka ta janye takunkuman da ta kakaba mata.
Jakadan Iran, a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa Iran, ba ta bukatar shiga wani sabon rikici da Amurka.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa hukumomin tsaron kasar da kuma gwamnatin jihar Neja kan rawar da suka taka wajen sako daliban Kagara da ƴan bindiga suka sace, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta ambato.
Shugaba Joe Biden, na Amurka na ci gaba da shan suka hatta daga bangaren ‘yan jam’iyyarsa ta demokrate game da kin daukar mataki kan yarima mai jiran gado na Saudiyya, wanda rahoton hukumar leken asirin Amurka ya bankado cewa shi ne ke hannu dumu dumu a kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi.
ABNA: Kasashen yammacin Duniya, sun shigo Niger. sun kasata zuwa al'umma da al'adu mabanbanta. ta yadda ba zasu iya hadu wa waje daya don su yake su ba. Hanyar yakar al'adun yammaci shine mu karfafa harsunan mu, na iye da kuma addinin mu, da al'adun mu.
All Content by AhlulBayt (a.s.) News Agency - ABNA is licensed under a Creative Commons Attribution 4.0 International License