JAWABIN RUFE TAFSIRIN AL- QUR’ANI NA BANA SHEKARA TA 1436/2015

  • Lambar Labari†: 701645
  • Taska : mu'assasatul thaqlain
NA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL KADUNA YUSUF SULAIMAN NE YA MAIDA SHI RUBUTU A’UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM BISMILLAHIR RAHMANAIR RAHIM WASALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIRIN

Mun godewa Allah Subhanahu wa Ta’ala wanda Ya nuna mana karshen tafsir na watan Ramadhan na wannan shekaran,wato shekara ta 1436 wanda ta dace da watan yuli 2015.Za mu ajiye karatu na tafsir na wannan shekaran,in Allah ya raya mu da lafiya har zuwa shekara mai zuwa zamu dora da izinin Allah a inda muka tsaya . Muna rokon Allah Ta’ala ya zama Ya bamu abin da Yake ba masu azumi da sallah a cikin wannan wata,muna fata ka da Allah Ya sanya mun ci abinci a wannan watan kamar yanda muka dinga ci a wajen Ramadhan .Muna fata Ya zama cewa ba mu yi barna na abinci a wannan watan fiye da yanda muke yi barna da abinci (Wal iyazu billah) a wajen watan Ramadhan . Na karanta bayanin wata Doktora a fannin abinci lokacin da take yin bayani ga Musulmi a wannan shekaran,kamar daga Niger take .Tana ce masu kada FASTING dinsu ya koma FEASTING wato ka da su bar azumin su ya koma gara da walima walima da biki da sauransu da sauransu.Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya kare mu daga azumin mu ya zama ashe FEASTING muka dinga yi ba FASTING ba.Muna fata Allah Ya gafarta mana Yayi mana rahma Ya kuma bamu albarka. Kamar yanda bama fata FASTING dinmu ya koma FEASTING wato azumin ya koma gara kawai haka ba ma fata Tafsir din da muke yi a cikin watan Ramadhan ya zama Takfir(kafirta Musulmi)har ya zama cewa Musulmi basu da tsanani a gaba a tsakan-kanin junansu da zagin junan su da kafirta junan su da jifan juna da tuhume tuhume masu tsananin gasken gaske ,basu da lokacin yin wadannan kaman lokacin Ramadhan har zama cewa Musulmi na yau da kullum Almajirai da mabiya su kosa watan ya fita ba domin sun gaji da ibada ba sai domin sun gaji da jin zage zage da soke soke da alfasha da ababen da sukayi kama da haka . Watan Ramadhan watan rahma ne,watan albarka ,watan gafara kuma Al-qur’anin da muke karantawa ya sauka ne a matsayin rahma, bai sauka domin masifa ba amma mu da kan mu in munga dama zamu iya maida wa ko jawo wa kan mu masifu da fitin-tinu kala-kala.Kofofin Aljannah a bude suke a watan Ramadhan kuma dukkan kofofin alkhairi a bude suke kuma a saukake sannan kofofin wuta a rufe suke a cikin watan Ramadhan,dukkan hanyoyin sharri an sa su suna da wahala a cikin wannan wata saboda haka duk lokacin da aka samu wani ya samu akasin abinda aka tanadi Ramadhan domin shi wannan shi ya jama kanshi wato shine Shaidanin kanshi ,shine kuma abokin gaban kanshi. A cikin wannan watan mun ji da’awowi masu yawan gasken gaske na kafirtawa wato Musulmi suna kafirta wadanda suka yi hukunci akan su daga cikin musulmi akan cewa su ba musulmi bane ba tare da la’akari da dokokin ridda ba da kuma sauran DAWAABIT DA MAWAAZIN na addini ba,kaman mafi girma daga cikin dokokin ridda shine mutum baya yin ridda bayan yayi Kalmar shahada saidai muna shakka akan ko yayi Kalmar shahadan ne,bayan mutum yayi Kalmar shahada baya yin ridda sai idan yayi inkarin DARURA a cikin DARURIYAT din addini da ijma’in dukkan musulmi gabaki daya ,wato rukunnai guda biyu ,dole ya zama abin da mutum yayi inkari ya zama Darura daga Daruriyat din addini.Sannan Malaman basu bari ba sai da suka yi bayanin abin da ake nufi da Darura,suka ce abin da ake ce ma Darura shine abin da aka sani cewa imani dashi rukuni ne ko asasi ne a cikin addini sannan suka kayyade da cewa dole ya zama dukkan musulmi sunyi ijma’i akanshi sai a ce mutum yayi ridda,ba abin da wani ya dauke shi darura ba,ba kuma abin da wani ya dauke shi ridda ba sai yayi wa mutum hukunci da ridda akai .Amma kaman misali inkarin Allah ko risala(sako) ko asalin wajibcin sallah ba rashin yin sallah ba ko inkarin asalin Hajji da irin wadannan ababen ko inkarin wani abu daga cikin addini wanda a ittifakin musulmi ridda ne to wadannan ake kira da Ridda ko a ce yayi Ridda.Daga baya ne aka samu wasu suka shigo suka dinga kawo kananan abubuwa da duk abin da suka ga dama ya yi masu suka yi sha’awan shi sai su ce mashi Ridda saboda haka sai ya zama suna kafirta mutane akan wannan asasin . Yana da muhimmancin gaske mu fahimci wannan cewa addinin Musulunci yana da sauki a shige shi amma yana da wahala a fita sannan shi wannan addinin yana da yalwan gasken gaske,ya fi kowa da kowa yalwa,ya fi zamani yalwa ,ya fi bigire yalwa sannan ya fi mutane gabaki dayan su yalwa,sannan kuma ayoyin shi suna karban fahimta daban daban sannan Akida ba guda daya bane sannan kuma fahimta a cikin Akida ba fahimta daya bace kuma bambamci a cikin fahimta baya kafirta Mutum.Misali:akwai inda Allah Subhanahu wa Ta’ala a cikin Alkur’ani yake cewa a suratun Nahal : BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM,WA ALALLAHI QASDUS SABILI WA MINHA JA’IR,WA LAU SHA’A LA HADAKUM AJMA’IN .ma’ana KUMA WAJIBI NE AKAN ALLAH MIKEWAN HANYA,KUMA DAGA CIKIN TA AKWAI KARKATATTA KUMA DA YA SO SHI ALLAH DIN DA SHIRYAR DAKU GABAKI DAYA. A nan wurin an samu Malamai sun yi gardaddami masu yawan gasken gaske a mustawa din Akida akan jingina hanya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala da kuma JA’AL wato ya zama Allah shi Ya sanya hanya din .Kaman Mu’utazila suka tafi a taqaice sosai cewa abinda aka jingina ga Allah shine QASDUS SABILI (wato hanya mikakka ) a ayan amma hanya da take JA’IRA ita wannan ba zaka iya jingina ta ga Allah ba wato ita Mustaqilla ce daban.Sai Ash’arawa suka yi masu raddi suka ce da hanya mikakka da hanya karkatatta dukkan su Allah Subhanahu wa Ta’ala ne ya halicce su amma abin da yasa ba a jingina hanya karkatatta zuwa ga Allah ba a wannan ayan shine saboda ladabi,sai wasu daga cikin Malaman Ash’arawa suka tafi akan cewa a’a dukkan su Allah Subhanahu wa Ta’ala ne Ya halicce su amma ita hanya mikakka din Allah Ya shiryatar da Mutane gare ta saboda karimcin shi ba don dole bane,wasu kuma suka tafi zuwa ga wasu ma’anoni da ra’ayoyi daban daban daga cikin Ash’arawa din.Amma Malaman Imamiyyah suka tafi akan cewa tabbas hanya wadda take mikakka itace wadda aka jingina ta ga izuwa ga Allah amma ita hanya karkatatta ba halittatta bace wato ba a halicce ta ba saboda ba hanya bace asasan,sakamako ne na kin bin hanya mikakka wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya sanya mutane akai sai ya zama sakamakon wannan ya zama akan karkatattan hanya amma a asali ba an halicce ta bane saboda haka mas’alan a jingina ta zuwa ga Allah ko ka da a jingina ta babu.Ta cikin wadannan guda ukun wane ne kafir ?Malaman Imamiyyah suka tafi akan cewa shi yasa Allah Subhanahu wa Ta’ala Yace WA LAU SHA’A LA HADAKUM AJMA’IN ,saboda wannan mikakkan hanya Allah Ya sa abi ta ne asasin zabi da ganin dama saboda mas’uliyyah da alhaki su tabbata akan wanda ya bi da wanda bai bi ba,saboda haka idan ka ga Mutane masu yawa basu bi hanya mikakka ba ba wai dan sunyi galaba akan Allah bane,Allah Ya so akan zabi za a bi hanya mikakka ne shi yasa Yace WA LAU SHA’A LA HADAKUM AJMA’IN ,to waye Kafir a cikin wadannan guda ukun ? Yana da muhimmancin gaske mutane su fahimta su fahimci wadannan al’amuran,su gane akan cewa zaburar da Gomnati akan ta kashe ‘ya’yanta ko ‘yan kasan ta ko ta hana su hakkoki na MUWADANA(CITIZENSHIP) wato na kasantuwa ‘yan kasa,wannan wauta ce babba kuma ba za tai nasara ba sannan ita Gomnatin idan ta karbi wannan zaburarwan to ita tafi wauta daga wadanda suka zaburar da ita din.Manzon Allah (saw) Ya wuce zamanin shi,lokacin da ya assasa tsarin mulki wanda majalisar dinkin duniya take kokarin da fahimce shi a yanzu a lokacin da ya je Madina bayan yayi hijira daga Makka zuwa Madina,yayi abubuwa na asasi masu muhimmancin gaske a matsayin matakan shi na farko na assasa hukumar shi ta Musulunci a Madina.Na farko,ya assasa Masallaci wato ya samar da wajen ibada sannan a lokacin da ba a ibada a cikin shi ya sa ana karatu da Adabi da koyon kira’an Alkur’ani da Fiqhu alkalanci da Ila akhirihi.Sannan Ya sanya dangantaka na ‘Yan uwantaka ta imani tsakanin Muhajirun da Ansar saboda Ya warware matsalan bambamci a sakafa tsakanin Mutanen Makka da Madina,sannan a cikin Mutanen Madina din Ya sasanta a tsakanin AUS da KAZRAJ.Sannan ban da haka Manzon Allah (saw) a mataki na uku Ya zama cewa Yayi yarjejeniya ta zaman lafiya tsakanin shi da Yahudun Yasrib wato Yahudawa daga Aus da Kasraj, Yayi yarjejeniya tsakaninshi dasu cewa su al’umma ne gabaki daya koma bayan wasun su , sannan Ya zo Yayi yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin Shi da Yahudawan Banu Qainuqa da Banu Quraiza da Banun Nazir saboda LA AQAL su din suna da ganin cewa suna akan Addini wanda suke bautawa Ubangiji guda daya sannan suna adawa da Nasara saboda haka sai suka ga ya dace su yi yarjejeniya tsakanin su da Manzon Allah (saw) akan asasin Muwadana (wato Citizenship).Wa nnan asasin shine duniya take kokarin ta koya wanda ta gina kasashen ta a kai wanda ake ce ma MODERN NATION STATES wato kenan dauloli na hukumomi na zamani a yau wanda wannan kuma za ka same shi Imam Ali (as) ya koye shi daga Manzon Allah (saw) a AHAD din shi ga Malikul Ashtar lokacin da ya aike shi zuwa ga Misr inda yake cewa ka sani cewa Mutane gabaki dayansu jinsu biyu ne :AKHUN LAKA FID DEEN da NAZIRUN LAKA FIL KHALQ ma’ana ko dan uwan ka a Addini ko kuma irin ka a halitta.Wannan sune Asulla na farko na MODERN NATION STATES wadanda aka kafa su yanzu akan asasin CITIZENSHIP wato akan asasin MUWADANA wato zaman kowa dan kasa mai hakki iri daya ba akan asasin Akida ba.Manzon Allah Ya wuce zamanin Shi lokacin da Ya assasa wannan tsarin mulki din kuma idan Mutum Ya dubi kasashe a duniya gabaki daya akan wannan asasin suke zaune kuma suke raye. Wannan International Passport dina ya jama’a,ina so in karanta maku abin da yake cikin shafin shi na farko.Kasashe a duniya a yau ba wai suna kare hakkokin ‘Ya’yan su bane a cikin kasashen su bane kawai har a ko’ina a duniya wato ko’ina dan kasa yake a duniya to kasar tana kare hakkokin shi kuma kowanene shi ba tare da la’akari da macece Akidar shi ba.A Passport din yana cewa :THESE ARE TO REQUEST AND REQUIRE IN THE NAME OF THE PRESIDENT AND COMMANDER –IN-CHIEF OF THE ARMED FORCES OF THE FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA ALL THOSE WHOM IT MAY CONCERN TO ALLOW THE BEARER TO PASS FREELY WITHOUT LET OR HINDERANCE AND TO AFFORD HIM OR HER EVERY ASSISTANCE AND PROTECTION OF WHICH HE OR SHE MAY STAND IN NEED ma’ana wannan munyi ne domin ku bukata sannan mu nema da sunan Shugaban kasa Commander in chief na rundunonin mayakan kasar Nigeria duk wani wanda wannan abin zai shafa (wato a ko’ina na duniya)su bar wanda yake dauke da wannan Passport din ya wuce kasar su cikin ‘yanci ba tare da sun tsonkwama mashi kuma ba tare da sun kawo mashi cikas ba kuma su bashi ko su bata ita duk wani taimako da kariya wanda shi ko ita ke bukata,kowane dan kasa kasa ke da wannan haqqin.Sannan a karshen Passport din rubuta cewa:IF LOST OR DESTROYED,THE FACT AND CIRCUMSTANCES SHOULD BE IMMEDIATELY REPORTED TO THE PASSPORT OFFICE,ABUJA OR NEAREST NIGERIAN MISSION OR CONSULATE AND TO THE LOCAL POLICE .NEW PASSPORTS CAN BE ISSUED IN SUCH CASES ONLY AFTER EXHAUSTIVE ENQUIARIES ma’ana Idan wannan passport din zai zama ya bace ko ya lalace,gaskiyar bacewar da kuma dalilan da suka sa ya bace din a yi gaggawa akai labarin zuwa ofishin passport a Abuja ko kuma ofishin Jekadanci mafi kusa a ko’ina a cikin duniya da kuma Police din kasar ko wurin.Ka ga yanda dan kasa yake da karfi da girma a wurin gomnati a kowace kasa kasa wadda ta san abin da take yi. To idan ya zama an sami wasu mutane a yau suna kiran Gomnati da Ta kashe ‘Yan kasar ta ko Ta hana su hakkokin MAWADANA (wato ta hana su hakkokin zama yan kasa),da su din da Gomnati in ta karbe su din za a yi masu hukunci da wauta da rashin sanin ya kamata ya rashin wayewa da rashin cancanta su rayu a cikin wannan zamanin na yau. Wa ya baka labarin cewa Addinin Musulunci kai aka aiko ka dashi ?ko kai aka ba amanan shi lokacin da Manzon Allah Ya tafi ?.Dukkan mu gabaki dayan mu ‘Yan Nigeriya ne,muna da hakkoki irin hakkokin kowa sannan akwai wajibobi akan mu kaman yanda akwai wajibobi akan kowa wato muna da hakkoki da wajibobi .Kuma a zamanin da muke a yanzu ya wuce a dinga INTIMIDATING din mutane ko a dinga BLACKMAILING dinsu ko ya zama cewa a dinga irin SCARE MONGERING ko abin da ake ce ma CRYING WOLF WHEN THERE IS NONE wato kenan bi ta da kulli ko firgita mutane ko tuhumce tuhumce ko ba mutane tsoro ko cewa akwai fitina a inda babu,wannan lokacin ya riga ya wuce. Sannan a matsayin mu na ‘Yan kasa muna da hanyoyi masu yawan gasken gaske da zamu iya yin amfani da su domin kare kanmu.Na farko,muna da Allah Subhanahu wa Ta’ala wato muna da Allah Azza wa Jal.Sannan na biyu muna da ababen da Allah Ya bamu su a wannan zamanin,Shi da kanshi ya bamu su :akwai hanyoyin kafafen yada labarai basu da iyaka ,akwai jaridu ,akwai gidajen Rediyo da Telebijin ,akwai wasiloli na AT- TAWASILUL IJTIMA’I wato Social Networking ,sannan ban da haka akwai kungiyoyi basu da iyaka a cikin kasa da kuma duniya gabaki daya na kare hakkin dan Adam ,sannan akwai kotuna ,saboda haka ba zamu kwanta muna bacci ba kowane Mutum Ya dinga tsammanin cewa zai iya tada mana da hankali ba,wannan lokocin ya riga ya wuce saboda haka mun ‘Yan Nigeriya ne yan kasa ne,sannan muna da kowanne hakki na Muwadana . Banda wannan ,ya kamata kowa ya gane in da bai gane ba cewa shi wannan Addinin na Musulunci da mutane suke gani ,wadanda suke riya sun san shi suke yin tafsiran Alqur’ani da abin da yayi kama da wannan,WHEN PUSH COMES TO SHOVE wato idan lokacin daukan mataki yayi za ta bayyana akan cewa daliban Alqur’ani ba su iya su zama balle har Malaman tafsirin Alqur’ani kuma Insha Allah PUSH din ya kusa zuwa SHOVE wato PUSH din WILL SOON BE DONE ,hakan za ta bayyana .Sannan su lura su dinga yi a hankali hankali saboda a littafan Musulmi gabaki daya akwai abin da yake daidai akwai abin da yake ba daidai ba,ba wani Ma’asumin littafin banda Alqur’ani a I’ITIQADIN mu saboda haka in muka fara fito da abubuwan da suke cikin littafai wadanda suke birnannu wanda mun fi so ya zama an bar su a birnannu din saboda idan muka fara fito dasu ido zai iya raina fata,THOSE IN GLASS HOUSES SHOULD NOT THROW STONES ma’ana wadanda suke zaune a gidajen kwalba (glass) ka da su jefa duwatsu wato bai kamata su jefa duwatsu ba saboda idan suka jefa duwatsu aka maido masu da martani da duwatsu to za su zama ba su da gidaje. Muna kira ga Gomnati ka da ta zama ta yi wauta ta saurari irin wadannan,wadanda ba abinda suke so in banda fitina cewa a kashe mutum domin ra’ayi ko kuma a hana mashi hakkoki domin ra’ayi,wannan ba dabi’an Manzon Allah bane,asasan ba dabi’an Annabi bace idan da sunan Annabi ake yi to ba dabi’an Annabi bace ,kuma ba SIRAN Annabi bace sannan KAD’AN ba dabi’an ASSALAFUS SALEH bace saboda ASSALAFUS SALEH ba haka suke ba,wani abu ne ba Addinin Musulunci ba .Kiran Hukuma ta kasha ‘Ya’yanta wannan ba karantarwan Addinin Musulunci bace,ku cire daga kwakwalen ku cewa Musulunci yace ayi haka. Bayan wannan,a iyakan mintinan da suka rage mana muna so mu yi godiya ga dabakoki na Mutane daban daban.Muna godiya asasan ga Allah Shi ba ya cikin jinsin Mutane,to muna godiya asasan ga Allah Ta’ala wanda Ya bamu kudra da lafiya wanda ta sanya muka dinga zuwa wannan wurin muna yin wadannan karance karancen har zuwa yau din mu dinnan,muna fata Allah Ya maimaita mana irin wadannan lokuta din masu yawan gasken gaske a cikin lafiya da wadata da shiriya da kwanciyar hankali .Muna godewa dukkanwadanda suka taimaka a wurin nasaran aiki wadanda muka yi a wannan wajen dukkan su gabaki daya da wadanda suka taimaka da kudaden su da wadanda suka taimaka a ayyuka da wadanda suka taimaka da karfin su da wadanda suke LOGISTIC da wadanda suka dinga zuwa nan gun suna karanta mana Alqur’ani kullum kafin mu fara tafsir da dabakoki daban daban da wadanda suka yi takaffulin abubuwan lantarki da sanyaya wuri da wadanda suka dinga bada abinci da wadanda suka dinga addu’o’i a darare da sauransu.Muna godiya ga gidan radiyon tarayya na Kaduna saboda karban bakoncin mu da kuma yada mana da kuma sanya mana tafsir din mu duk da yake ba kyauta bane .Muna godiya daga farko ga Alhaji Abba Zayyan Zonal Director na Federal Corporation of Nigeria Kaduna,muna cewa BY AND LARGE ON THE WHOLE wato in aka kalla yanda aka tafiyar da tafsir din wannan shekaran a radiyon gabaki daya kaman an samu cigaban inganci sosai ta bangaren sauti da bangaren rashin samun matsala lokacin da aka yin tafsir din da kuma ta bangaren nisa a zango da abubuwa masu yawan gasken gaske.Muna fata in DIGITILIZATION ya zama ya karu wato a cigaba da IMPROVING dinshi har ya zama cewa ana yiwa mutane hidima kamar yanda ya kamata.Sannan muna godiya ga Alhaji Yusuf Dan Audi wanda yake shine Assistant Director na Marketing ,sannan muna godiya ga Malam Hasan Muhammad Sani (Controller na Marketing ) muna godiya KAD’AN ga PRODUCER din mu wanda LAILA NAHAR ya dinga kai komu don ya tabbatar cewa karatun namu yana kaiwa gidan Rediyon kuma ana sa mana akan lokaci wato Malam Ibrahim Muhammad Rigasa Allah subhanahu wa ta’ala ya saka mashi da alkhairi,sannan muna godiya ga wadanda suka dinga hada sauti a shirye shiryen kamar su Ahmad Alhasan Dankurmi,kamar su Agnes Sylvanus ,kamar su Victoria Duru ,kamar su Bala Sa’idu Chori .Sannan muna godiya ga Continuity Announcers wadanda su suna da yawan gasken gaske suna shift da lokaci zuwa lokaci to dukkansu gabaki dayan su kowanne daya daya daga cikin su ko da ambaton suna ko ba ambaton suna mun gode masu Allah Ya saka masu da alheri ,Allah Ya basu abin da yake ba masu kyautatawa . Muna godiya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala Mujaddadan,muna fata Allah Ya kaimu shekara mai zuwa da shekaru masu zuwa masu yawan gasken gaske domin ya zama cewa Yana lullube mu da alherai wadannan shekarun.Sannan muna cewa: BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN ,ARRAHMANIR RAHIM ,MALIKI YAUMID DIN ,IYYAKA NA’ABUDU WA IYYAKA NASTA’IN ,IHDINAS SIRADAL MUSTAQEEM,SIRADAL LAZINA AN’AMTA ALAIHIM ,GAIRIL MAGDUBI ALAIHIM WALAD DAALIN ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMADIN WA ALI MUHAMMAD RABBANA INNAKA TA’ALAMU MA NUKFI WAMA NU’ULIN ,WAMA YAKFA ALAIKA MIN SHAI’IN FIL ARDI WALA FIS SAMA’I RABBANA ALAIKA TAWALKALNA WA ILAIKA ANABNA WA ILAIKAL MASIR ALLAHUMMA INNA NAS’ALUKAL HUDA WAT TUQA WA AFAFA WAL GINA RABBANAG FIR LANA WALI IQWANILALLAZINA SABAQUNA BIL IMAN WALA TAJ’AL FI QULUBINA GILLAN LILLAZINA AMANU RABBANA INNAKA RA’UFUR RAHIM RABBI AUZI’INI AN ASHKURA NI’IMATAK AL LAZIY AN AMTA ALAYYA WA ALA WALIDAY WA AN A’AMALA SALIHAN TARDAH WA ASLIH LI FI ZURRIYATIY INNI TUBTU ILAIKA WA INNIY MINAL MUSLIMIN ALLAHUMMA KUN LI WALIYYIKA HUJJATU BIN HASAN SALAWATUKA WA ALA ABA’IHI FI HAZIHIS SA’ATI WA FI KULLI SA’A WALIYAN WA HAFIZAN WA QA’IDAN WA NASIRAN WA DALILAN WA AINAN HATTA TUSKINA HU ARDAKA DAU’A WA TUMATTU’UHU DAWILA BI RAHMATIKA YA ARHAMAR RAHIMIN ALLAHUMMA QAD AMARTA NA BI DU’A’IKA WA WA’ADTA NA BIL IJABA FA QAD DA’AUNAKA KAMA AMARTA NA FASTAJIB LANA KAMA WA’ADTANA INNAKA LA TUKLIFUL MI’AD ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALI MUHAMMAD.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni