ALKUR’ANI BA RUWANSHI DA WANI WAI NAKA SAI NAKA __ Cewar Sheikh Halliru Maraya
cigaba ...-
-
Hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da Murna _____Inji Sheikh Yakubu Yahaya Katsina
Yuli 23, 2017 - 12:30 AMYau Asabar 22 ga watan Yuli 2017 ne,Fudiyya Tahfiz Kano ta yi bukin yaye dalibai mahaddata Alkur’ani a filin Dantata dake Dandishe Kano. Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako a wajen bikin ya bayyana cewa hardace Alkur’ani ga yara abin farin ciki ne da murna. Malamin yayi nasiha da jan hankali ga daliban da suka haddace Alkur’anin da kuma Malaman su daliban.Sannan ya nuna muhimmancin samar da makaranta ta tafsirin Alkur’ani mai girma domin ka da a bar yaran su tafi haka nan don sun yi sauka. Sannan ya tabbatar da cewa a cikin rahoton da turawan mulkin mallaka suka kaiwa iyayen gidansu,akwai cewa yankin gabas (Borno)wuri ne da ake samun ilmin Alkur’ani shi yasa ake neman tarwatsa yankin.Yanzu ta bayyana karara ana fada da Alkur’ani ne,sannan ita kuma hukuma tana so ta kashe tasirin karatun Alkur’ani a cikin al’umma. Malamin yayi kira ga mawadata a cikin harka da su taimaka ma makarantun Fudiyya,yana cewa: “Su Malam na fada mana cewa mutum ya kure iyakar abinda yake iya yi domin neman sakamako a lahira.” Ya kara da cewa: “Su Sayyida sun bada lakani cewa idan kana bayarwa (wato infaqi) to Allah zai nunnuka maka abinda kake bayarwa din.” Sannan Malamin ya kirayi ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da suyi ilimin boko amma lokaci guda kada a bar ilimin Alkur’ani domin dukkansu ilimi ne kuma ana yin ilimi domin Allah ne.Yana cewa: “Shi karatu ana yinsa domin Allah ne,idan aka cire Allah a cikin karatu,to,komai sai ya dame ma mutum.” A karshe yayi kira da ‘yan uwa su hada kansu yana cewa: “Mu kara riko da junan mu,mu girmama ra’ayin juna.Duk ayyukanmu na gayya ne,duk inda muke mu yiwa juna uzuri.A iya sani na babu wani dan uwa wanda yake wani aiki don rugujewar harka,kowa na yin iya kokarinsa domin cigaban harka.” Bukin ya samu halartan wakilan ‘yan uwa na garuruwa da dama da sauran ‘yan uwa daga sassa daban daban na kasan nan.
cigaba ... -
Baje Kolin Kur'ani Na Kasa Da Kasa A Tehran
Mayu 30, 2017 - 7:42 PMAn bude baje kolin kur'ani mai tsarki na kasa da kasa karo na 25 a birnin Tehran na kasar Iran, tare da halartar madaba'antu na cikin gida da kuma na kasashen ketare.
cigaba ... -
Gasar Kur'ani Ta Duniya A Tehran
Afirilu 20, 2017 - 10:49 PMAn shiga rana ta biyu a gasar kur'ani ta duniya da aka bude a jiya a birnin Tehran na kasar Iran a babban dakin taruka da ke babban masalalcin marigayi Imam Khomeni.
cigaba ... -
JAWABIN RUFE TAFSIRIN AL- QUR’ANI NA BANA SHEKARA TA 1436/2015
Yuli 21, 2015 - 1:50 PMNA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL KADUNA YUSUF SULAIMAN NE YA MAIDA SHI RUBUTU A’UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM BISMILLAHIR RAHMANAIR RAHIM WASALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYIBINAD DAHIRIN
cigaba ... -
Il Sacro Corano
Maris 8, 2013 - 12:00 AM
- 1