Hirar Jaridar Almizan da Sayyid Madamasi Yakubu, kanin Sheikh El-Zakzaky

  • Lambar Labari†: 754890
  • Taska : Harkarmusulunci a Nigeria
Brief

Sunana Badamasi Yaqoubu. Kuma Uwarmu daya, Ubanmu daya da Malam Ibrahim Zakzaky. Ni nake bin sa. Mahaifinmu ya rasu ya bar mu, mu 16 ne. Takwas maza, takwas mata. Allah ya kaddara mu bakwai ne muka rayu a wajen Mahaifiyarmu. Wato wadanda muke Uwa daya, Uba daya, mu bakwai ne. Sauran tara din,

ALMIZAN: Da farko za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatun mu.

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Sunana Badamasi Yaqoubu. Kuma Uwarmu daya, Ubanmu daya da Malam Ibrahim Zakzaky. Ni nake bin sa. Mahaifinmu ya rasu ya bar mu, mu 16 ne. Takwas maza, takwas mata. Allah ya kaddara mu bakwai ne muka rayu a wajen Mahaifiyarmu. Wato wadanda muke Uwa daya, Uba daya, mu bakwai ne. Sauran tara din, ’yan wasu dakin ne. Mahifiyarmu ta haifi ’ya’ya 12 ne.

ALMIZAN: Waye Shaikh Ibraheem Zakzaky?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: To, Malam Ibraheem mutum ne haziki, mai basira, kuma mai kwakwalwa. Mutum ne mai hakuri da ibada. Mahaifinmu Malami ne kuma manomi. Kuma bai sa ka a cikin layin masu zuwa gona, sai in ba ka sauke Alkur’ani, ka shiga littattafai ba. Akwai yayyin Malam guda biyu; Malam Abdulkadir da Malam Sani, suna gaba da shi a Alkur’ani. Idan an biya masu karatu sukan manta, amma Malam ne yake tuna masu, tunda a gabansa ake biya masu. Gaskiyar magana, ya kamata Yayyunmu su ce Malam Ibraheem Malaminsu ne. Saboda hazakarsa yana koya masu karatu, tare da cewa bai kai su ba.
 Tare da cewa Mahaifinmu Malami ne, amma yana tura mu makarantu. Misali mun yi karatun Allo a makarantar Sarkin Ladanai, Malam Mani, da Malam Sani Abdulkadir. Shi kuma Malam Ibraheem ya yi karatu a wajen Malam Sani Na’ibin Zazzau, Malam Ibrahim Nakakaki, Malam Isa Namadaka (Kawu). Lokacin da ya je School For Arabic Studies (SAS) ya yi karatu a wajen Malamai uku. Gidan Shaikh Nasiru Kabara, Gidan Shaikh Isa Waziri da kuma Limamin Yola.
 Ba wani littafi da ake karantawa a cikin Mazhabar Malikiyya, wanda Malam Ibraheem bai karanta shi a gaban Malami ba. Ba wani littafi na lugga wanda ake yi, wanda Malam bai yi shi a gaban Malami ba.
ALMIZAN: Ya za ka bayyana alakar da ke tsakanin ku da Malam?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Kamar yadda na ce ne, Uwarmu daya, Ubanmu daya. Ni nake bin sa. Kuma Malam, Malamina ne, ina karatu a wajensa. Muna da kusanci sosai da shi. Ku ma za ku iya gani, kullum muna tare da shi. Duk lokacin da aka kama Malam akan kama tare da ni. In ma ba a kama da ni ba, ni nake fara zuwa wajensa. Tare da cewa tsakanin mu bai fi shekaru uku ba, amma ina daukar Malam a matsayin Uba, kuma Malamina.
ALMIZAN: Kamar watanni biyar da suka gabata akwai wasu abubuwa da suka faru, inda sojoji suka kai hari gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky suka kashe mutane sama da dubu, ciki har da ’ya’yanku bakwai da kuma Yayarku, bayan sun kama Malam din. Ya kuka ji wannan abu da ya faru?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Wannan abin da ya faru, abu ne mummuna kwarai da gaske. A ranar Asabar din da aka kawo wannan harin, muna tare da Malam har wajen karfe 9:00nd. Na dawo gida misalin karfe 10:00nd, sai na fara jin karar harbe-harbe a Gyallesu, dama sun kai hari Husainiyya Bakiyyatullah tun da rana. Wannan harin da aka kai ya sa ni da iyalina ba mu yi barci ba saboda wadannan abubuwan da ke faruwa. Washegari na yi yunkurin komawa Gyallesu, amma sai ya zama babu hanyar da zan shiga, Sojoji sun tare ko’ina.
 Daga abubuwan da na ji sun faru, lallai na fahimci cewa wadannan mutane sun zo kashe Malam ne. Kuma gaskiyar magana sun kashe Malam din, Allah Madaukakin Sarki shi ne ya kaddara cewa bai kashe Malam ba, don ya nuna masu, shi ne mai kashewa, mai rayawa. Amma duk wani makami da ka sani wanda ake yaki da shi tsakanin kasa da kasa, har ma da wadanda aka haramta yin amfani da su, kamar makamai mai guba, wallahi sun yi amfani da su a gidan Malam, gidan farar hula. Don tabbas sun yi amfani da makami mai guba.
 Inda suka harbi Malam, da irina ne, ko irin wani aadi, lallai mutuwa ya kamata ya yi take, domin duk inda suka harbe shi ba inda zai rayu ba ne. Alal misali akwai wurare uku da suka harbe shi; sun harbe shi a hannun hagu, wanda yake harbi ne kamar guda hudu, sun yi rugu-rugu da hannun. Kirji suka yi niyyar harba wajen zuciya, sai Allah ya kau da shi. Sun harbe shi a fuska, harbi biyu. Goshi suka yi niyyar harba, sai Allah ya kautar da ita. Sannan sun fatattaka katarensa na dama, sai da naman kafar ya zube. Da za a yi masa aiki, sai da aka yanko naman kafar hagu aka yi ciko da shi. Dama kamar yadda masana suka fada shi ne; ka’idar harbin katare, jini bai tsayawa. Dama in ka ga an harbi mutum a katare, an harbe shi ya mutu ne, ana jiran jininsa ya tsiyaye ne ya mutu. Kuma haka suka yi wa Malam.
 Domin bayan sun harbe shi din, sun fito da shi sun ajiye shi a waje, don jinin ya gama tsiyayewa. A lokacin da suka fito da shi suka ajiye shi a waje, wani Soja ya zo ya yi masu tsawa, yana cewa; “Ku dauke shi ku je a tsai da jininsa. Domin in kuka bari wannan mutumin ya mutu, to mun shiga uku”. Amma haka har ya je ya dawo ya sake yi masu magana, amma ba su dauke shi ba. Suna so jinin nasa ya gama tsiyayewa ya mutu.
 Daga bisani sun dauke shi a wata mota ‘ambulance’ suka shiga gudu da shi, suka tafi da shi depot. Zainab ’yar gidan Alhaji Hamid Danlami ta bi su tana kuka tana cewa su sake shi. Sai wannan babban nasu ya zo yake ce mata; “Ai za mu je a tsai da jininsa ne. Ai ba za mu bari wannan Malamin ya mutu ba, mun san in mun bari ya mutu mun shiga uku”.
 Wannan maganar sojan ta saba da ta wanda ya harbi Malam ya fada masa. Domin shi cewa ya yi; “Mun zo ne mu kashe ka, kuma mu kashe Shi’a”. Ka ga shi bai boye ba. Yana fadar haka ne bayan ya harbi Malam din da wadanda suke tare. Shi ne Malam din yake fada a cikin zuciyarsa cewa, da ana kawo karshen Shi’a da kisa, da an kawo karshen ta da kashe Imam Husaini (AS).
 Harbin da suka yi masa a hannu ba hannun suke nufi ba. Gaskiyar magana kirjinsa suke nufi, kuma kirjin ya nufa, Allah ne kawai ya tsai da harbi a hannu. Kuma inda suka harbe shi a fuska, ba fuskar suka yi nufi ba. Sun yi nufin ragargaza kansa ne. Sai Allah ya tsai da ita a ido. Kuma inda suka harbe shi a katare, sun harbe shi ne jininsa ya gama tsiyayewa. Wannan masanin harbi ne yake fada min haka.
ALMIZAN: Da yake kun samu zuwa wajen Malam har sau biyu, kuma kun yi magana da shi a waya kamar sau hudu. Masu karatunmu za su so su ji a wane hali kuka same shi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Gaskiya ziyararmu ta farko da muka kai wa Malam ita ta tabbatar mana da yana raye. Ita ziyarar farko da muka kai, kamar wata uku ke nan da suka gabata. Lokacin da muka je gaskiyar magana ya soma samun sauki. Mu biyar muka je. Da ni, Kanwarmu Hajiya Maimuna, Suhaila, Zainab da Sajida. Wadannan uku na karshe, an yi waki’ar suna tare da Malam, don haka yana zaton sun mutu, shi ya sa na ce duk su zo mu je don ya gan su. 
ALMIZAN: To, a wane hali kuka same shi a zuwan ku na farko?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Mun same shi ya soma jin sauki. Mun tarar an yi masa aiki a hannu. Amma hannun bai motsi. Na fuska kuma, kamar misalin idon hagunsa yana rufe da bandeji. Sannan idon dama da shi yake gani, shi ma an yi masa aiki, an yi wani ciko a ciki. Ita kuma kafarsa ta dama, kamar yadda na fada maka a baya, katare aka harba, sai aka yanko naman kafar hagu aka yi ciko. Yadda wajen ya fafe yana bukatar ciko. Don haka ita ma kafar tun daga kugu har kasa an sanya mata bandeji.
ALMIZAN: To ita kuma wannan ziyarar da baya-bayan nan fa, a wane hali kuka same shi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: To ita wannan ziyarar da muka kai kamar makwannin biyu da suka gabata, gaskiyar magana ita ce, komai ya warke. Kuma hatta tafiyar Malam, ba dingishi. Yana tafiya ne ba tare da sanda ba. Hannun ma an kwace, yana amfani da shi. Ido ne kawai ya rage. Amma yana gani tangaran da na dama, shi kuma na hagu, za a yi masa aiki a makon farko na wannan watan na Bature a Lagos. Kodayake aikin zai shafi duka ido biyu ne. Irin harbin da suka yi wa Malam bai kamata ya zama Malam yana tafiya da sanda ba, sai dai ya zama ana gungura shi ne a keken guragu. Domin hannu da kafar ya kamata a yanke su ne, amma cikin ikon Allah sai ga shi duk sun warke.
ALMIZAN: Ita kuma Malama Zeenat ya kuka same ta?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Malama Zeenat kamar yadda na fada a wajen taron Yaumus Shuhada, ko ma wancan zuwan farko da muka je, na ce ita fa Malama ta samu lafiya dari bisa dari. Ta kara warkewa ne a wannan zuwan. Misali a wancan zuwan na ga cewa in ta ce maka an harbe ta a hanci, bayan harbe-harben da aka yi mata, za ka yi mamaki. Domin wajen ya warke.
 Gaskiyar magana harbin da aka yi wa Malama ya fi na Malam yawa. Domin ita Malama abin da ta yi, bayan duk ’yan uwa wadanda ke katabus an gama da su, sai ya zama daga Malam sai su. Sai take ganin da a zo a kashe mijinta tana gani, kamar yadda aka kashe ’ya’yanta uku a gabanta, gara ita ma a kashe ta kafin a kai kan sa. Saboda haka sai ta ba da kariya, ta ba da rayuwarta. Da ita da Suhaila da Zainab da Sajida sai suka kare Malam domin kar harsashi ya same shi. Shi wannan Sojan da ya shigo inda su Malam din suke, bindiga mai jigida yake da ita. Haka ya bude masu wuta yana harbin su, kuma harbin daidai cikin Malama ne. Cikin ikon Allah duk harbin da ya yi mata, sai ya zama harsasan Allah ya tara su a bangaren dama. Su kansu jami’an tsaron sun tabbatar min cewa an cire mata harsasai ne, ba harsashi daya ba. Sannan na ga hijabinta ta bangaren hagu ya yi fata-fata. Akwai wani harbin da ya yi mata a baya, wanda yake har yanzu tana da wannan harsashin. Sun ce cire wannan harsashin zai zame mata matsala. Harbin da ya yi mata a fuska, wanda ya same ta a hanci, shi ne ya sa ta fadi. Lokacin Malam yake shaida mata cewa shi ma fa an harbe shi. Ko da ta duba sai ta ga Malam jina-jina.
Gaskiyar magana Malama Zeenat ta fi shan harsashi fiye da Malam, sai dai raunukan Malam sun fi yawa, sun fi muni. Wani abu da zai tabbatar maka komai karewar Allah ne, da Suhaila da Zainab ba harsashi daya da ya same su. Duk wannan luguden wuta da ya yi bai same su ba. Amma ita Sajida harsashi ya same ta a haba. Bisa ikon Allah bai shiga ba, don da ya shiga da ya fasa makogwaronta. Ita kuma Suhaila sun sa kotar bindiga sun bubbuge ta. Har yana zagin ta cewa wai ta yi kama da Ubanta, ba ta jin tsoro. Duk abin da suka yi Suhaila ta ji tsoro, ba ta tsorata ba. Ta kangare masu. Sai da suka kama ta suka bankare ta ta baya suka daure ta suka bubbuge ta suka sanya ta a mota.
ALMIZAN: Su kuma ’ya’yan Malam uku ya aka yi aka kashe su?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Su wadannan yara guda uku, an harbe su ne a gaban Mahaifinsu. Misali Hammad a gaban Malam aka yi daga-daga da kansa. A goshi suka harbe shi. Shi ma Ali kamar sauran ’yan uwansa ya amshi izini a wajen Malam ya fita. Yana cewa ba amfanin rayuwarsa tun da ba Malam. Ali ya juya zai fita waje ya tari Sojoji, sai wani ya biyo ta baya ta harbe shi a keya. Shi ma daga-daga ya yi da kansa kwanya ta fito. Shi ma na Humaid abin tausayi, yanka shi suka yi da harsashi. Harbin da suka yi masa, yadda ka san an yanka rago. Wato irin harbin da suka so su yi wa Sajida. Shi ma a gaban Malam aka yi masa haka.

ALMIZAN: Kamar yadda aka saba ganin Malam cikin shiga ta kamala, da rawani da alkyabba da kuma manyan kaya, jama’a za su so su ji yadda kuka same shi a wannan ziyarar da kuka kai masa ta baya-bayan nan?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Yadda ka san yanayin shigar sa haka muka gan shi. Na ga kun buga wani rubutu a ALMIZAN da wani dan uwa da muka je da shi, wato Gamawa ya yi, inda ya bayyana cewa ya ga Malam yana tafiya bayan an zo da jeep an bude ya fito. Ya gan shi da rawani da abaya da komai da komai. Lallai wannan haka ne.

ALMIZAN: Jama’a na hasashen cewa ko bayan da Malam da Malama, akwai wasu ’yan uwan da ake tsare da su a tare, ko kun ji wani abu mai kama haka?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: A gaskiya mu dai mun ji an ce su biyu din ne kawai a wajen. Da Malam ne da Malama, ba wani.
ALMIZAN: A farkon haduwarku da Malam, za ka iya tuna abin da ya fara fada maku, ko kuma ya tambaye ku?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Magana ce mai tsawo, tun daga lamarin gida da kuma abubuwan da suka faru. Alal misali zuwana wancan ya tambaye ni Malam Abdulhamid Bello da Malam Mansur Gumel da kuma wasu mutane da yawa, wadanda yake tsammanin sun yi shahada. Wadanda suka yi shahadar na fada masa, wadanda kuma ba su yi ba na shaida masa suna nan. Amma gaskiya ya yi mamakin jin cewa Malam Abdulhamid Bello da Malam Mansur Gumle suna nan da rai.
 To a wannan zuwan ma da muka yi ya sake tambayata, su Malam Abdulhamid Bello da Mansur Gumle din. Yana tunanin ko na boye masa ne a wancan karon. Na ce masa gaskiya Malam suna nan da rai.
Ya tambayi wasu, wadanda muke da lambobinsu, sai mu hada shi da su su yi magana. Misali ya yi magana da mutane da yawa, daga cikin su har da Shaikh Saleh Lazare. Sun yi magana da shi ta minti 15-20. Akwai Alhaji Ali Babba, sun yi magana da shi a waya, saboda batun auren Muhammad.

ALMIZAN: Akwai mutane da ya san sun yi shahada tun kafin a tafi da shi ko, kamar su Shaikh Muhammad Turi da sauransu, na ji an ce har ya fadi yadda za a yi da su ko?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Haka ne. Ya san wadannan.

ALMIZAN: Ya samu labarin ba a ba da gwawwakin ’yan uwa ba?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Ya samu labari. Wani abin mamaki ma shi ne; tun kafin ya samu labarin cewa ba a ba da gawawwakin ’yan uwa ba a wajen su Farfesa Dahiru Yahya da suka riga mu zuwa, Malama Zeenatu ta yi mafarkin cewa ba a ba da gawawwakin ’yan uwa ba, sai ta gaya wa Malam mafarkin da ta yi. Wannan abin ya bai wa Malam mamaki. Sai ga su Farfesa Dahiru Yahya sun tabbatar masa ba a ba da gawawwakin ba. Sai mu ma da muka je muka kara tabbatar masa. Ko wannan zuwan da muka yi ya tambaye mu, muka ce masa har yanzu ba a bayar da gawawwakin ba.

ALMIZAN: Ko akwai wani sako da ya ba ku?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Lallai ya fada mana cewa duk abin da ake yi a ci gaba, kar komai ya tsaya. Sawa’un Yaumu Shuhada ne, Nisfu Sha’aban ne, Kudus ne, Ta’alimomi ne, Muzaharori ne, ko wasu tarurruka ne. Duk abin da ake yi na Harka a ci gaba da yi kar a fasa. Hatta abin da Malam ya saba yi na raba wa mutane kayan Azumi, wallahi ya yi umurnin a yi kar a fasa. Ina fatan ’yan uwa su san haka. Malam ya ce duk wadanda yake bai wa kayan Azumi, lallai a je a ba su kar a fasa.

ALMIZAN: Da yake cikin watan Rajab kuka je, na ji an ce kun same shi yana Azumi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Dama Malam ya saba da wannan Azumin. Fiye da shekaru 40, Malam yana Azumin watannin uku ne a jere, da Rajab, Sha’aban da kuma Ramadan. Bai shan ruwa sai Shawwal. Tun da Malam ya wayi gari ya ga Mahaifinmu yana yin wannan Azumin na watannin uku a jeren, bai fasa ba. Ka’idarsa ne, da zarar Rajab ya kama, Mahaifinmu bai sake cin abinci da rana, sai Shawwal. Tun a wancan lokacin Malam Ibraheem yake wannan Azumin tare da Mahaifinmu. Tun da ya soma yi, har gobe bai daina ba. Don haka duk da wannan halin da yake ciki bai sa ya daina ba. Mun same shi yana Azumin Rajab.
Da yake mun san Malam yana son yin buda baki da ruwan Zamzam, shi ya sa muka tafi masa da shi. Kuma yana zuwa abin ya fara tambayar mu ke nan. Akwai ruwan Zamzam? Muka ce akwai. Kodayake mun san wanda muka kai masa ba zai ishe shi ba, muna fatan nan gaba za mu sake aika masa.

ALMIZAN: A wancan karon kun je ku biyar ne, a wannan karon fa?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Wannan karon ya nunka wancan. Ban da wadancan mutanen da muka je da su a zuwan farko, akwai karin mutane, kamar akwai Muhammad dan Malam din, Dahaltu, Malam Abdulrahman Yola da Malam Muhammad Gamawa. Mun shiga muna tare da Malam tun karfe 2:30 har karfe 6:30. Ka ga an dade sosai.

ALMIZAN: Ya kuka gan shi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Yadda ka san Malam yana nan yadda yake. Ko shi ma Gamawa ai ya fada cewa yadda ya san shi haka ya gan shi, yana magana kamar ana zaman falo a Gyallesu. Ya gan shi da dukkan kamala.

ALMIZAN: Akwai wasu da suke ganin kamar Malam ya canza, saboda irin harbin da aka yi masa?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Yadda yake haka yake. Ba wani abu da za ka gani yanzu a jikinsa illa raunin da suka yi masa a ido na hannun hagu. Shi ma kuma ana ta kokarin a yi masa magani.

ALMIZAN: Na ji an ce yana karatu yana rubutu ko?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Sosai kuwa. Mun je masa da littattafai kuma yana karance-karance ba tare da gilas ba. A gabanmu ya rubuta wasu addu’o’in da ke cikin littafi, ya kuma rubuta wasika.

ALMIZAN: A wannan harin da Sojoji suka kai, bayan kashe ’ya’yan Malam da sauran ’yan uwa, akwai kuma Yayarsu da ita ma suka kashe. Za ka fada mana yadda aka yi suka kashe ta?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Lallai haka ne akwai Yayarmu Hajiya Binta ta je gidan Malam din. Tsawon dare har zuwa wayewar garin ranar Lahadi muna ta magana da ita. Har zuwa lokacin da na buga wayar sai na ji wani mutum ya dauka. Sai na ke cewa na ji an ce Sojoji sun shigo gidan? Sai na ji wannan mutumin ya ce a’a. Wannan maganar sai na fahimci lallai wannan mutumin Soja ne, kuma ya dauki wayar Binta ne.
 Yadda labari ya tabbata gare mu shi ne; ta fito suka harbe ta a kafa, tana tare da wata Sista da ake kira Malama Shema’u, amma ita ba su harbe ta ba lafiyarta kalau. Sai suka tura su a wani daki suka banka masu wuta. Har ita Binta din tana ce masu; “Za ku kona mu ne da wuta da ranmu? Da wuta za ku yi mana azaba?” Tana cewa; “Ku bar ni in gana da dan uwana kafin ku kashe ni”. Ba su bar ta ba. Malam yana jin maganarta, amma ba yadda zai yi, domin shi ma yana cikin wani hali. Saboda haka bayan sun harbe ta a kafa, sai suka kona su da ransu.

ALMIZAN: Jama’a na mamaki, duk da wannan abu na kashe ’ya’yanku da ’yan uwanku, amma sai aka ji wani a cikin gidanku yana cewa ya yi farin ciki da abin da aka yi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Ba ka rasa dan Adam da samun mai kiyayya ko mai hassada. Idan ka lura tarihi ne yake maimaita kansa. Annabi Adamu ya samu da Kabilu, wanda ya fandare masa. Annabi Nuhu ya samu da Kan’ana, wanda shi ma ya fandare masa. Annabi Yusuf ya samu kansa da kiyayyar ’yan uba. Wannan da yake cewa ya yi farin ciki da wannan kisan gillar da aka yi wa ’ya’yanmu da ’yan uwansa, Ubanmu daya ne. Ka ga an kashe ’yan uwa sama da 1,000, ciki har da ’ya’yan Malam uku, da na Malam Abdulkadir daya, wato Shamsuddeen da kuma Yayarmu, Hajiya Fatima, wacce aka fi sani da Goggon Kaura, amma duk da haka yake cewa ya yi farin ciki.
Wannan da yake magana Ubanmu daya ne, wato Malam Sani, duk da cewa yana kungiyar Wahabiyyawa ne, wato dan Izala ne. Amma in ka lura ka hada maganarsa da ta Malam Abdulkadir, wanda shi ma dan Izala din ne, za ka ga akwai bambanci tsakanin maganar wanda muke Uwa daya, Uba daya da kuma wanda muke Uba daya. Akwai kuma kaninmu, shi ma dan Izala ne, ya tausaya mana sosai. Babu abin da ya sa wannan, illa hassada da ’yan ubanci.

ALMIZAN: Amma mutane suna ganin tunda shi ma Malami ne ya san illar kashe rai ba tare da hakki na shari’a ba kuma ga ’yan uwantaka, yaushe kuma zai goyi bayan haka?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Babu mamaki don wani mutum ya fadi haka. Idan ka lura ’ya’yan Annabi Yakubu suna da ilimi, wasu ma suna cewa Annabawa ne, amma ka ga irin kiyayyar da suka nuna wa dan uwansu Annabi Yusuf. Saboda haka duk wanda yake mamakin abin da shi wannan dan uwa namu ya fada, ka ce masa ya karanta Suratul Yusuf, amsarsa na wajen. Haka kuma Annabi Muhammad (S) ya samu Abu Lahabi da Abu Jahal. Don haka don Malam ya samu wannan, yana kara tabbatar mana cewa lallai shi Magajin Annabawa ne.

ALMIZAN: Na san ku ’yan uwansa za ku fi kowa jin takaicin wadannan maganganun?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Wannan haka yake. Amma ai ga Malam Abdulkadir, duk da cewa dan Izala ne, amma ka ji abin da ya fada. Haka kuma akwai mu da kani sunansa Yahya Yaqoub; shi ma da za ka je ka yi hira da shi, ba zai nuna maka irin wannan kiyayyar ba, duk da kuwa shi ma dan Izala ne. Saboda haka wannan ba wani abu ba ne, duk wani mai kira yana haduwa da irin wannan. Shehu Usmanu ya samu irin wannan ’yan ubancin. Har yake cewa shanu ne suka kare masa yake da’awa. Don haka don mun samu dan uwa ya yi mana haka, ba wani abin mamaki ba ne.

ALMIZAN: Kun samu labarin kafa Hukumar Binciken kisan kiyashin da sojojin suka yi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Na samu labari. Amma wannan Hukumar Binciken da aka kafa, kai da gani ka san ba za ta yi adalci ba. Na farko Sojoji ne suka aiwatar da wannan kisan. Sojoji ba suna karkashin Gwamna ba ne, suna karkashin gwamnatin Tarayya ne. Na biyu da aka kafa wannan Hukumar, babu dan uwa ko daya a ciki, alhali su Sojojin nan da suka yi wannan kisan akwai su a ciki. Kuma a cikin mambobin Hukumar akwai makiya, akalla an nuna masu guda uku a ciki. Daya daga cikin su ya rubuta littafi ya ce a kashe ’yan Shi’a, a kakkama su. Yaushe za ka sa ran samun adalci a wajensu?
Idan ana son Hukumar da za ta yi binciken gaskiya, gwamnatin Tarayya ce za ta kafa, kuma a sanya mutanen da ba su da hannu a ciki, wato ’yan ba-ruwanmu, wadanda za su yi adalci, don a hukunta wadanda ke da hannu a ciki.
 Ka je ka samu mutane ka bude masu wuta, ka yi amfani da dukkan karfinka, sannan ka kama su ka je ka daure su, ka kama Jagoransu bayan kuma kun fadi cewa kun zo kashe shi ne. Wani Soja ya fada cewa son zo kama Malam ne, ko kashe shi. Kuma abin da suka yi ke nan. Sai kuma ka zo ka kafa Hukumar Bincike ba tare da kama daya bangaren ba?
 Ya za a yi Gwamna ya kafa Hukumar Bincike, bayan kuwa shi ma kansa daya ne daga cikin wadanda suka hannu a cikin wannan lamarin. Ya yi rushe-rushe, ya yi maganganu hatta a wajen kafa Hukumar Binciken. Ya nuna masu yadda za su gudanar da bincike da irin abubuwan da ake so su gano. Don haka kaurace wa wannan Hukumar shi ne ya fi.

ALMIZAN: Kun bai wa Shaikh Zakzaky labarin kafa wannan Hukumar?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Lallai ya samu labari. Kuma matsayinsa shi ne a kaurace mata. Abin da Malam ya fara cewa shi ne Soja nawa aka kama? Muka ce ko daya. Ya ce mu aka kashe, mu aka kama, mu aka yi wa rushe-rushe, kuma mu aka kafa wa Hukumar Bincike. Ya ce kar a je. Wannan shi ne matsayin Malam.

ALMIZAN: Gaba daya ya za ka bayyana wannan abin da ya faru?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Wannan abin da ya faru gaba daya, tarihi ne yake maimaita kansa. Meye bai faru ga Annabawa da kuma A’imma ba? Mu dauki Imam Husaini (AS) a matsayin misali, irin haka ta faru gare shi, bayan an kashe ’ya’yansa, shi ma aka kashe shi. Don haka ta faru ga Malam ba wani abin mamaki ba ne, tarihi ne yake maimaita kansa. Kuma duk wanda ya rike hanyar gaskiya, sai ya hadu da irin haka. Kamar yadda ya zo a cikin Suratul Bakara, Allah ya ce zai jarabce mu a kan dukiyarmu, rayukanmu da ’ya’yanmu. Imam Ali (AS) yana cewa ko dutse ne a cikin ruwa yana son mu, sai ya hadu da jarabawa. Manya-manyan darajoji na tare da manya-manyan bala’o’i. Za su iya kashe mu, amma ba za su iya kashe addini ba.       

ALMIZAN: Daga karshe akwai wani sako da kake da shi?

MALAM BADAMASI YAQOUBU: Kiran da nake da shi ga ’yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky su ci gaba da biyayya da kuma bin Na’ibin Jagoran, wato Malam Yakubu Yahya Katsina, wanda yake tafiyar da jagoranci Harka. Dole ne ya zama muna tafiya a karkashin jagoranci. Mu tuna fa muna da makiya, suna so su shigo mu, suna so su tunzura wasu a cikin mu su dauki matakin da bai kamata ba. Don haka wajibi ne mu zama masu bin umurni da kuma yin komai bisa tsari kamar yadda aka san mu da shi.
’Yan uwa su kara dagewa da Salloli da kuma addu’o’i. Muna ganin tasirin addu’o’in nan da ake yi. Mu bi umurnin da ya zo daga wajen Malam Yakubu Yahya.


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

asura-mystery-of-creation
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky