$icon = $this->mediaurl($this->icon['mediaID']); $thumb = $this->mediaurl($this->icon['mediaID'],350,350); ?>

SHAIKH HAMZA LAWAL; TATTAKI ZUWA ZARIA YA HALASTA

  • Lambar Labari†: 721984
  • Taska : mu'assasatul thaqlain
HALASCIN TATTAKI DAGA GARURUWA ZUWA ZARIYA DOMIN KAMA DA SAHABBAN IMAM HUSAIN (AS) DA KUMA JAJANTAWA YAN UWA MASU TATTAKI DAGA KANO ZUWA ZARIYA NA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL

Babu dalili a doron kasa kuma babu dalili a sararin samaniya wanda ya halatta abin da ya faru na harin bom akan masu tattaki daga Kano zuwa Zariya,in har haka ya farun,daga Kura zuwa Dakatsalle,a iyakar ma’alumat din da suka zo mana.Wa’yanda suka aikata in sun aikata da gaske ba su daga cikin jinsin mutane na hakika,kila suna da siffa irin ta mutane amma haqiqanin su ba haqiqanin mutane bane.Sannan dole ne ya zama cewa mutum ya tausawa wa’yanda abin ya same su in har haka din ya faru,sannan kuma yayi fatan Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi masu abin da yake saka wa na mafi kyawun sakamakon da yake yi wa bayin shi. Yawancin lokuta mutane suna husuma akan tattaki,cewa ya halatta ko bai halatta ba?Tattaki bil khusus wanda ake yi a Nigeriya.Mutane sun ta yin kokari su san ra’ayin mu akan tattaki da ake yi daga garuruwa zuwa Zariya. Ra’ayin mu a takaice a yau akan wannan kujeran shine ya halatta.Tattaki daga wani gari zuwa Zariya domin yin kama da Sahabban Husain (as) ya halatta,amma babu dalili akan kasantuwar shi MUSTAHAB.Abin da nake nufi da lugah ta yau da kullum shine cewa babu dalilin da ya hana wato ya halatta.Haka  kuma ba mu da dalili wanda ya haramta tafiya daga wani gari ka zo Zariya domin yin kama da mutanen Husain (as),shi yasa ya zama MUBAH(wato ya zama halas),me yasa ya zama halas?Babu dalili akan HURMA kuma rashin dalili akan HURMA wannan dalili ne akan IBAHA(halasci) amma ba dalili bane akan ISTIHBAB,shi kafin ya zama MUSTAHAB  ba dole sai akwai NASSI wanda yake akan tafiyyan bil khusus ba,in akwai NASSI AMM wanda yace a dinga irin wannan tafiyar domin kama da Imam Husain to sai ya zama wannan ta shiga wannan dalili din AMM,to ba mu dashi,ba mu da dalili Amm akan mustahabbantar da yin tafiyan,wato mustahabbantarwa da ma’anar akwai lada akai.To amma akwai halacci saboda babu nassi,ta yaya ya zama Halal ?Saboda KULLU SHAI’IN LAKA HALALUN HATTA TA’ALAM ma’ana ko menene wato dukkan komai ya halatta sai ka san ya haramta wato HATTA TA’ALAMUL HURMA FA TATRUKAHU,saboda haka ya halatta wato JA’IZ ,MUBAH amma ba mu da dalili akan ISTIHBAB. Ba muna yi ne don mu gamsar da wani ba,ko don wani ya yabe mu ko wani ya zarge mu,duk daya suke da zargi da yabo a mas’aloli na isar da sakon Allah Subhanahu wa Ta’ala wa’yannan duk daya ne a wurin mu.Saboda haka ba muna so bane ka yabe mu ko muna so ka zarge mu,ba tanan bane,sashen abin da muka fadi wanda yayi maka dadi ba ma bukatar ya ma,sannan sashen abin da muka fadi wanda bai ma dadi ba ya baka haushi ba ma bukatar zargin ka domin ba zai mana tasiri ba. Saboda haka babu dalili a doron kasa sannan babun dalili a sararin samaniya wanda ya inganta abin da aka yi in an yin a tsakanin Kura da Dakatsalle,sannan wadanda suka aikata suran su  suna iya zama suran mutane amma a waqi’in su ba waqi’in mutane ba.Wa’yanda aka kashe su an kashe su IN COLD BLOOD.Mutum na da hakki yai tafiya in da ya ga dama a cikin Nigeriya ko a ko’ina a cikin duniya,duk inda ka ga dama kuma kowa yana da hakkin yai akidar shi  wato ko da a ce bai halatta suyi tafiyar ba nake so nace sai suka yi baka da hakkin ka zo ka sa masu bom.Sannan kuma in aka rama to?yaya kenan?zai zama akwai FAUDA.Mu an karantar damu HIFZUN NIZAM wato kare nizami,bin doka da oda saboda haka bai kamata wani yayi farin ciki ba akan abin day a faru akan wa’yanda suke yin tafiyan saboda kila wai ka saba dasu.Mun saba dasu a wasu lokaci  amma akan STRATEGY da EMPHASIS amma ba mu saba dasu akan MABADI’I ba,ba mu saba dasu akan AHDAF  ba,mun saba ne akan wasa’il kila,sannan kuma mun yi tarayya dasu akan akida,kuma wannan ba hari ne wanda aka kaima masu akan ZAWAT din su ba,an kai hari ne akan akidan da suke misaltawa,in ba a gane wannan ba,ya kamata a gane a yau ko kuma yanzu,kuma zai iya samun kowa,saboda haka muna tausaya masu sannan kuma muna fatan Allah Ta’ala ya saka wa wa’yanda ya shafa,wadanda suke a matsayin DAHAYA na wannan harin. Muna da TAHAFFUZAT akan ababen da sukan yi wani lokuta wato muna da tsokaci da walakin akan wasu ababe amma ba akan shi tattakin ba domin shi akan shi ya halatta,kila ababen dake kewaye dashi da kuma wasu abubuwa daban a wajen tattakin,zaka iya cewa muna da ra’ayi akai amma ra’ayin namu bai da kima saboda ra’ayi ne akan harshen nasiha amma ba dole ya zama yana da kima ba,wa’yannan din kila muna dasu da ra’ayoyi da mulahazozi akan wadannan ababen amma dai ba akan asalin tattakin ba saboda ba mu da dalili akan haramci. Mutane sun ta surutu akan wannan,mutane sukan muhimmantar da abin da bai shafe su ba,tun da ba wanda yace maka dole ka zo kayi ko ya wajabta maka kayi,mutane ne suka dora wa kansu kuma suna yi,bai shafe ka ba.Amma kila inda zai shafe ka in ka hadu dasu akan hanya suka tilasta maka sai kayi,kuma kila haka zai iya faruwa ko su ajiye ka a wuri daya na mudda mai tsawo cewa ba zaka wuce ba sai sun gama wucewa,wato ka’idoji na zamantakewa muna da TAHAFFUZAT akan wannan.Sannan muna da TAHAFFUZAT akan kirkire kirkire da kage kage  wa’yanda makaryata a cikin su-Tabbas kowacce al’umma akwai makaryata,in baka yadda ba kana nufin dukkan ku ma’asumai ne –In baka yarda a cikin ku akwai makaryata ba da wadanda suke yi ba don Allah ba da  sauran da sauran su ba ba zaka cigaba,kamar masu da’awan cewa tun kafin yau sun ga bom a karkashin gada,ko sun yi kaza kaza da irin wadannan,akwai da’awowi kala kala masu yawa wadanda zaka ga suna yi,kila muna da Tahaffuzat akan wadannan amma akan asalin tattaki ba.Ba mu taba yadda akan cewa akai masu hari ba saboda sun kare titi ba,saboda ai Redeemed Christian Church of God sun yi taron sun a karshen shekara a Lagos kwana biyu akayi a mota ba gaba ba baya ,kuma a ko’ina ana yin haka,kiristoci da musulmi da yan siyasa da kowa da kowa.In ana so a hana gabaki daya,ba wai a shakkasa wasu mutane ba,sannan su ma din abin da ya kamata.Ya kamata in an gan su a ga Husain (as) wanda suke yi domin shi,ya kamata idan aka gan su sai a ga Husain. Bai dame mu ba ko wani ya ji haushi ko ya ji dadi ba.In suna yi ya kamata a ga Husain,suyi abin da suke yi,ka dasu ce sunan shi MUSTAHAB saboda kafin abu ya zama MUSTAHAB dole sai ya zama akwai NASSI AMM ko KHAS,wato dole ya zama akwai dalil ala kulli hal.Amma shi MUBAH ya wadatar ya zama babu hani ko kace HURMA AMM ko KHAS,suna cewa –wannan ba sai mun shiga wannan ka’idar ta USUL ba-ya zama MUBAH.Babu wani Malami wanda zai ce maka da AL-HUKMUL AWWALIY ya haramta sai ya haramta maka da AL-AHKAM ATH-THANAWIYYA,kamar wannan abin da ya faru misali,don shi wani Malami zai iya haramtawa amma ba don asalin shi ba.Sannan MUBAH shine abin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bar ka kayi amfani da hankalin ka,shine abin da Shahidus Sadar yake ce ma : “MANDAQATUL FARAG “ wato BLANK SPACE da Allah Ta’ala ya baka ko BLANK AREA wato wurin da yake Holoko wanda ya baka yana so ya ga hankalin ka,anan gurin ya wajabta ya mustahabbantar a wannan gefen sannan a dayan gaefen ya haramta ya karhantar sannan a tsakiya kuma ya bar ka yana so ya ga hankalin ka kuma wannan da’iran tana da yalwa.To shine  ake so aka hankalin ka a wannan wurin shine ma’anar MUBAH,Mubah shima uslubi na tarbiyya.A takaice ba ina so in shiga bincike bincike na fiqhu da sauran su bane,amma wannan shine ra’ayin mu dangane da tashin bom da aka yi in ya tashi din,duk maganar da ba wannan ba da sunan mu,ba mu muka fadi,ya fadi ne a madadin kan shi kuma yana da yanci yayi ta’abiri akan ra’ayin shi saboda demokradiyya ake Nigeriya.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*