• Gaskiyar Abunda Ya Faru A Muzaharar Kaduna

    A ranar juma’ah,29 ga watan Ramadan da ta gabata ne ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky suka bi sahun sauran mutanen duniya wajen amsa kiran Imam Khomaini na shirya gangami da muzaharori da taruka domin nuna goyon baya ga raunanan duniya musamman Palasdinawa,da kuma bayyana irin zalunci da ta’addancin sahayona akan al’umma. Wani shedan gani da ido ya shaida mana cewa masu muzaharan sun fito ne daga wajen Polytechnic dake Tudun Wada Kaduna zuwa wajen Kasuwan Barci suna rera wakoki na goyon baya ga Palasdin da kuma kira ga gwamnati da saki Sheikh Zakzaky ,da misalin karfe 1:00 da wani abu,sai kawai suka ga gamayyan ‘yan sanda da sojoji suka fara harba tiyagas da harsashai masu rai akan wa’yannan masu muzaharan. Kanar Kingsley Umoh,mataimakin daraktan hulda da jama’a na rukuni na daya na sojojin Nigeriya ya tabbatar ma da wakilinmu cewa an kama kimanin mutane goma,amma yace sojoji sun je wajen ne bayan ‘yan sanda sun daidaita lamurra. Wani daga cikin wadanda aka yi wannan muhazaran ya tabbatar mana da cewa suna cikin gudanar da muhazaran Quds din lami lafiya cikin tsari,sai kawai gamayyan ‘yan sanda da sojoji a daidai shatale talen kasuwan barci suka fara bude masu wuta da harsashai masu rai da antayo barkonon tsohuwa akansu,su kuma masu muzaharan suna jifansu da duwatsu.Daga nan ne ‘yan sandan suka gayyato ‘yan iskan gari dauke da nau’i iri iri na makamai suna bin su da sara da doka. Wani shedan gani da ido(bai so a ambaci sunansa) ya tabbatar mana da cewa ya ga wata mata da aka fasa mata kai sakamakon duka da kokara,sannan an harbi yaron Dr Mustafa Sa’ida mai suna Husain wanda bai wuce shekara 9 ba.Babu tabbacin rasa rai kaman yanda wannan malamin ya shaida mana. Sannan mun samu labarin kama wani dan jarida dake wakiltan gidan rediyon jamus a lokacin wannan yamutsi amma an sako shi bayan kungiyar ‘yan jarida ta Kaduna ta je ta bi lamurran,amma ‘yan sandan sun bugaci da ya koma ofishin su domin bin bahasi ran laraba mai zuwa. Jiya asabar da yamma wasu gungu na matasa na harka sun kara fita muzahara da nufin karasa wannan muzahara da basu kammala ba ran juma’a saboda hari da aka kai masu.Sun yi muzaharan ne daga shatale talen Leventis dake tsakiyan Kaduna kuma Alhamdulillah sunyi sun gama lafiya ba tare da wani abu ba

    cigaba ...
  • Hujjar Fatimatu Zahra{A.S} kan Lamarin Fadak

    Yayin da suka hana Zahra (a.s) hakkinta, sun nemi ta kawo shedu cewa Fadak tata ce, babu wani da take da su sai Hasan da Husain da Imam Ali (a.s), sai dai mutanen ba su yarda da su a matsayin shedu ba tun da mijinta da 'ya'yanta ne.

    cigaba ...