Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti
31 Disamba 2022
Gwamnan Lardin "Asiut" na Masar Ya Karrama Daliban Kur’ani 140 da suka nuna kwazo
Gwamnan Assiut na kasar Masar "Essam Saad" ya karrama dalibai maza da mata 140 na wannan lardi da suka samu matsayi na farko a gasar "Tajvid, Azan da Abtahal Dini" a yayin wani biki.
31 Disamba 2022
Kasashen Larabawa sun soki kalaman Macron na kyamar Musulunci
Kalaman shugaban Faransa game da addinin muslunci ya haifar da martani daga wasu kasashen larabawa da wasu kungiyoyi suka yi kira da a kaurace wa kayayyakin Faransa.
31 Disamba 2022
Hadin kan malaman musulmi na adawa da matakin Taliban na hana mata ilimi
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Hossein Ebrahim Taha, ya bukaci hadin kan malamai da hukumomin addini na duniya kan matakin da kungiyar Taliban ta dauka na hana 'ya'ya mata ilimi.
28 Disamba 2022
Tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan Shi'a a Zariya Najeriya 2015
A shekarar 2015 ne sojojin Najeriya suka kashe daruruwan mutane ta hanyar kai wa 'yan Shi'ar kasar hari a yankin Zaria.
27 Disamba 2022
Halartar mutane daga kasashe 80 a gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 39 a Iran
Yayin da yake bayani kan ayyukan kwamitoci daban-daban na gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 39, shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani ta MDD ya bayyana cewa: Bayan shekaru takwas da aka yi, adadin kasashen ya zarce 70, ya kuma kai 80.
27 Disamba 2022
'Yan IMN Sun Halrci Tarukan Bikin Kirsimati Domin Karfafa Zaman Lafiya Tsakanin mabiya Addinai A Najeriya
'Yan kungiyar IMN sun halarci taron bikin kirsimeti a wata majami'a domin taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Isa (AS).
25 Disamba 2022
Sheikh Al-Azhar: Gaisuwar Idin kirsimati ga Kiristoci ta dogara ne akan koyarwar addini
Sheikh Al-Azhar ya bayyana cewa taya kiristoci murnar bukukuwansu ba wai yabo da bukukuwa ba ne, sai dai a bisa koyarwar addini, ya kuma bayyana cewa kin taya kiristoci murnar bukukuwan da suke yi ba shi da alaka da Musulunci.
21 Disamba 2022
Minista a Kenya ya kare hijabin da mata musulmi suke sakawa
Aden Duale, ministan tsaron kasar Kenya, ya goyi bayan sanya hijabi da mata musulmi ke yi a kasar, yana mai cewa al'adun musulmi sun nuna cewa matansu su sanya hijabi a bainar jama'a.
20 Disamba 2022
Shahadar wani fursunan Bafalasdine sakamakon rashin kula da lafiyarsa a gidajen yarin Yahudawan mamaya
Fursunonin kungiyar Falasdinu sun sanar da shahadar Nasser Abu Hamid a wani asibitin kasar Isra'ila sakamakon rashin kulawar likitocin da hukumomin gidajen yarin yahudawan sahyoniya suka yi.
20 Disamba 2022
Sojojin Siriya 2 sun jikkata a harin da 'yan sahayoniya suka kai a Damascus
Sojojin Siriya 2 ne suka samu raunuka sakamakon harin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai a wajen birnin Damascus a safiyar yau Talata.
19 Disamba 2022
Taron musulmi da kirista na Amurka tare da karatun ayoyin kur’ani
Kungiyar musulmi da kiristoci a jihar Indianapolis ta kasar Amurka sun tattauna batutuwan da suka shafi addinan biyu tare da gudanar da taron addu'o'i na hadin gwiwa a wani taron ibada na shekara shekara.
19 Disamba 2022
Gasar cin kofin duniya ta Qatar ta kawar da farfagandar kyamar Musulunci da kafafen yada labaran Yamma ke yadawa
Wani kwararre a nahiyar Afirka ya ce nasarar gudanar da gasar cin kofin duniya da Qatar ta yi ya kalubalanci yunkurin kasashen yammacin duniya na nuna bakar hoto na musulmi; Hoton da ya kasance yana danganta musulmi da ta'addanci da rashin zaman lafiya.
18 Disamba 2022
Karatun Kur’ani Daga Ma’aikacin Hubaren Imam Hussain A Gaba Paparoma
An watsa faifan bidiyo na karatun "Osameh Al-Karbalai", fitaccen makaranci na hubbaren Hosseini a Karbala, a gaban Paparoma Francis, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, a yanar gizo.
17 Disamba 2022
Tafsirin Alqur'ani na farko da harshen Albaniya
“Fathi Mahdiou” kwararre ne a fannin ilimi kuma shi ne cikakken mai fassara kur’ani na farko da harshen Albaniya a kasar Kosovo, wanda ya yi tsokaci kan tsarin tarjamar kur’ani mai tsarki a yankin Balkan a cikin littafinsa da aka buga kwanan nan cikin harshen Larabci.
16 Disamba 2022
Kiran da Hamas ta yi na yin gagarumin gangami a Masallacin Al-Aqsa
Kakakin kungiyar Hamas a birnin Kudus ya yi kira da a gudanar da babban taron al'ummar Palasdinu a masallacin Al-Aqsa domin dakile makircin mahara a lokacin bukukuwan Hanukkah na Yahudawa.
16 Disamba 2022
Karatun musamman na matashi mai tilawa na Masar
Bidiyon karatun na musamman na Mohammad Jamal Shahab, matashin mawakin Masar, ya samu karbuwa sosai a shafukan sada zumunta na Masar.
16 Disamba 2022
Rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan gwamnatin Sahayoniya a shekarar 2022
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoto da ke cewa Falasdinawa 150 da suka hada da kananan yara 33 ne suka yi shahada a hannun dakarun yahudawan sahyoniya tun daga farkon shekara ta 2022, inda ta bayyana wannan shekara a matsayin shekara mafi muni ga Falasdinawa.
15 Disamba 2022
An amince da kudurin kawo karshen shigar Iran cikin kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan mata
An amince da kudurin cire Iran daga kwamitin kula da harkokin mata na Majalisar Dinkin Duniya da kuri'u 29 da suka amince da shi, 8 suka ki amincewa, 16 kuma suka kauracewa zaben.
14 Disamba 2022
Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta tabbatar da alhakin harin da aka kai kan ayarin man Iran
Babban hafsan hafsoshin gwamnatin yahudawan sahyoniya ya sanar a hukumance cewa kai hari kan motocin dakon man fetur na Iran a kan iyakokin kasashen Siriya da Iraki aiki ne na wannan gwamnati.
14 Disamba 2022
Ministan harkokin wajen Yemen: Iran ita ce kasa daya tilo da ta goyi bayan al'ummar Yemen
Ministan harkokin wajen kasar Yemen ya yaba da irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take baiwa al'ummar kasar Yemen a tsawon shekaru na yaki.