Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti
1 Faburairu 2024
Ci Gaba Da Murnar Zagayowar Makon Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran
Iran: Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Tarukan Raya Ranar Da Imam Khumaini (r.a) Ya Dawo Gida Mai Albarka
A karshen watan Disamba, labari ya bazu na aniyar Imam Khumaini na komawa Iran. Duk wanda ya ji labarin idanunsa sun ciko da kwalla na kewarsa. Al'umma sun sha wahala shekaru goma sha hudu suna jira. Duk da al'umma da magoya bayansa sun kasance cikin damuwa da tashin hankali kan rayuwar Imam Khumaini, kasancewar har yanzu gwamnatin sojan da ke biyayya ga Shah tana kan karagar mulki. Don haka abokan Imam suka ba da shawarar a jinkirta tafiya kadan don samar da sharuddan da suka dace don kare shi.
31 Janairu 2024
Shin Ko Makomar Amurka A Vietnam Tana Jiran Gwamnatin Sahayoniya A Gaza?
Halin da gwamnatin Sahayoniya ke ciki a wannan zamani a fili ya yi kama da irin shigar Amurka a yakin Vietnam.
31 Janairu 2024
Bidiyo Da Hotunan Yadda Sojojin Yaman Su Kai Tattakin Don Muna Goyon Bayaan Falasdinu
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku bisa nakaltowa daga kamfanin labarai na IRNA cewa: sojojin kasar Yaman sun gudanar da tattaki domin nuna goyon bayansu ga Falasdinu wanda wannan Tattakin soji na sojojin kasar Yemen yana kunshe da hafsoshi 3,600 daga dakarun kiyaye zaman lafiya na dakarun tsaron fadar shugaban kasa an gudanar da shi acikin tazarar kilomita 130 da nufin kara shiri da tallafawa Falasdinu.
30 Janairu 2024
Sheikh Zakzaky: Al'ummar Najeriya Sun Fara Sanin Mazhabar Ahlul Baiti (AS) Shekaru 44 Da Suka Gabata.
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, yayin da yake ishara da yadda Nahjul-Balagha da Sahifa Sajjadiyya suka yawaita a cikin al'ummar kasar Najeriya da kuma halartar sama da mutane miliyan 5 a cikin jerin gwanon na Arba'in, ya ce: sanin mutanen Najeriya da mazhabar Ahlulbaiti. Al-Bait (AS) ya fara ne shekaru 44 da suka gabata, kuma kafin wannan lokacin babu Shi'a ko daya a Najeriya, wannan abin mamaki ne!.
30 Janairu 2024
An gudanar Da Taron Bikin Karrama Shaikh Zakzaky HF A Birnin Qom Na Kasar Iran
Labarai Cikin Hotuna Na Taron Bukin Karrama Shaikh Zakzaky Da Aka Gudanar A Birnin Qom Na Kasar Iran
30 Janairu 2024
Bidiyo | Cikakken Rahoto Kan Jirgin Ruwan Sojan Amurka Da Sojojin Yaman Suka Kai Wa Hari
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA ya habarta cewa: an fitar da cikakken rahoto kan jirgin ruwan sojan Amurka mai suna "Lewis B. Puller", wanda ke bayar da cikakken goyon baya da taimakawa ga 'yan ta'addan yahudawan sahyoniya wanda kuma sojojin Yaman suka kaiwa harai a cikin tekun bahar maliya.
30 Janairu 2024
Majalisar Dinkin Duniya: Farin Yunwa Ya Tabbata A Zirin Gaza
Michael Fakhri", wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan abinci, ya ce: "Yunwa a Gaza ta zama babu makawa bayan da wasu kasashe suka dakatar da taimakon kudi ga Hukumar ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA).
30 Janairu 2024
Ma'aikatan Gwamnatin Amurka Da Yawa Zasu Gudanar Da Yajin Cin Abinci Domin Nuna Goyon Bayan Gaza
Wakilan kungiyar sun shaidawa jaridar Guardian cewa "Mambobin za su shirya wani yajin cin abinci na kwana daya a ranar Alhamis, domin mayar da martani ga yadda Isra'ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki ta hanyar hana abinci shiga zirin Gaza".
30 Janairu 2024
Tare Da Sakon Ayatullahi Makarem Shirazi;
Za A Gudanar Da Bikin Kaddamar Da Sabbin Ayyukan Wiki Na Shi'a
Tare da halartar Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya sakon Ayatullah Makarem Shirazi; Wiki Shia za tai bukin buɗe sabbin ayyukanta guda biyu.
28 Janairu 2024
MSF: Babbar Cibiyar Lafiya Ta Gaza Ta Ruguje A Cikin Hare-Haren Isra'ila
Manyan kungiyoyin kiwon lafiya sun buga kararrawa kan rugujewar muhimman ayyukan kiwon lafiya a cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza, a daidai lokacin da Isra'ila ke kai hare-hare ba kakkautawa a Khan Yunis da ke kudancin Gaza.
28 Janairu 2024
Hizbullah: Za Mu Mayar Da Martani Ta Hanyar Fadada Zango Na Hudu Da Karfi Mai Inganci
Sheikh Naim Qassem Yayin jawabin da ya gabatar a wajen bikin kaddamar da littafin "Hukunce-hukuncen Shugabanni da Ma'aikata" (الوصايا العلوية للمديرين والعاملين) na (Imam Khamenei, hafizahul lahu), yayi bayanin cewa "ana gani laifin kungiyar Hizbullah da gwagwarmaya a Labanon saboda sun sauke wajibin da ke kansu."
28 Janairu 2024
Labarai Cikin Hotuna Na Bikin Maulidin Imam Ali (AS) A kasar Ghana.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - Abna ya habarta cewa, an gudanar da bukukuwan maulidin Amirul Muminin (a.s.) bias daukar nauyin "Muhammad Abujaja" wakilin majalissar Ahlul Baiti (a.s.) wanda aka gudanar a kasar Ghana, tare da halartar gungun masoya Ahlul-baiti As, a cikin babban masallacin wannan kasa.
28 Janairu 2024
Jirgin Ruwan Birtaniyya Da Aka Kai Wa Hari A Tekun Bahar Maliya Na Dauke Ne Da Man Da Isra'ila Ke Anfani Da Shi Wajen Kai Hare-Haren Bam A Gazza
Jirgin Ruwan Birtaniyya Da Aka Kai Wa Hari A Tekun Bahar Maliya Na Dauke Ne Da Man Da Isra'ila Ke Anfani Da Shi Wajen Kai Hare-Haren Bam A Gazza
28 Janairu 2024
Labarai Cikin Hotuna Na Bikin Taklifi Na Yara mata A birnin Nabul kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya bayar da rahoton cewa: an gudanar da bikin fara ayyuakan takilfi ga wasu gungun ‘yan mata daga birnin Nabal da ke lardin Aleppo a yankin Halab a daidai lokacin zagayowar ranar da aka haifi Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) a ranar Lahadi bias daukar nauyin Majalisar Ahlul-Baiti (S) ta Siriya. Babban mai jawabi na musamman a wannan biki shi ne Hujjatul-Islam Wal Muslimeen Muhammed Jaza
27 Janairu 2024
Labarai Cikin Hotuna: Na Mummunan Yanayi Na Rayuwar Miliyoyin Mutanen Da Suka Rasa Matsugunansu A Gaza Cikin Sanyi Da Ruwan Sama Da Dusar Kankara
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya kawo maku hotuna na irin mummunan yanayi na rayuwar miliyoyin mutanen da suka rasa matsugunansu a gaza cikin sanyi da ruwan sama da dusar kankara
27 Janairu 2024
Martanin Jigajigan Yahudawan Sahyoniya Kan Hukuncin Kotun Duniya:
Bin Ghafir: "Kotun Hague abin kunya ce" bai kamata kotun Hague ta ya yarda ta saurari tare da yanke hukunci da zai zamo illa ga ci gaba da wanzuwar gwamnatin Isra'ila.
27 Janairu 2024
Kungiyar Hizbullah Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Kan Matsugunan Yahudawan Sahyoniya
Majiyoyin labarai sun bayar da rahoton cewa da safiyar Asabar din nan ne aka kai hare-haren rokoki da kungiyar Hizbullah ta kai kan sansanonin sojojin yahudawan sahyoniya da ke arewacin Palastinu da ta mamaye.
27 Janairu 2024
Wace Ce Alƙaliyar Kotun Hague Da Ta Ke Goyon Bayan Isra'ila?!
ai shari'a Julia Sebutinde, 'yar kasar Uganda ce mai shari'a wadda ta yi wa'adi na biyu a kotun kasa da kasa bayan sake zabenta a ranar 12 ga Nuwamba, 2020. Wacce ita ce kuma shugaban jami'ar Royal Muteesa ta Masarautar Uganda a halin yanzu.
27 Janairu 2024
Labarai Cikin Hotuna: 'Yan Shi'ar Kasar Rasha Sun Gudanar Da Bukin Maulidin Amirul Muminin (AS) Tare Da Halartar Mataimakin Mai Kula Da Harkokin Kasa Da Kasa Na Majalisar Ahlul Baiti (AS).
- ABNA 24 - ya habarta maku cewa: an gudanar da maulidin Amirul Muminin (a.s.) a Husainiyar Imam Ali (a.s.) a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha. Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen "Muhammed Ali Muinian" mataimakin shugaban harkokin kasa da kasa na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya halarci wannan taron inda ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron tare da gabatar da kyautar banar Ahlulbaiti ta wannan majalisa zuwa ga Husainiyyar Imam Ali (A.S.).
27 Janairu 2024
Dr. Hassan Sadeghian, Shugaban Commonwealth da Turkiya na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) shi ma ya halarci zaman.
Labarai Cikin Hotuna An Gudanar Da Zaman Makokin Wafatin Sayyida Zainab (A.S) A Birnin Darband Na Kasar Rasha Tare Da Halartar Jami'an Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya.
ABNA 24: an gudanar da zaman makokin wafatin Sayyida Zainab (a.s) a masallacin "Hamshahri" da ke birnin "Darband" a yankin Dagestan na kasar Rasha. Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen "Muhammed Ali Muinian" mataimakin shugaban harkokin kasa da kasa na Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya halarci wannan zama inda ya gabatar da jawabi kan matsayin Sayyida Zainab (S) kuma ya bada kyautar banar majalisar Ahlulbaiti ga masallacin Hamshahri.