Iran Za ta Maida Martani Akan Sabon Takunkumin Amurka Akanta

  • Lambar Labari†: 796566
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Tsawaita Takunkumin Amurka Akan Iran,zai fuskanci martani

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Ya ce; Tsawaita wa'adin takunkumin da majalisar dattijan Amurka ta kakabawa Iran zuwa shekaru 10, zai sa Iran din ta maida martani.

Dr. Ali Rarijani ya kara da cewa; Da akwai hanyoyi da dama da Iran din za ta iya maida martani da su.

Shugaban na Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kara da cewa wasu sassan na takunkumin da majalisar dattijan Amurkan ta kakabawa Iran din suna cin karo da yarjejeniyar Nukiliya.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai majalisar Amurkan ta amince da tsawaita takunkumi akan Iran na wasu karin shekaru 10 masu zuwa a nan gaba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky