Ayatullahi Jannati: Kiyayyar Amurka Kan Iran Ya Sabawa Dokokin Kasa Da Kasa

  • Lambar Labari†: 796557
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Shugaban Majalisar Kwararru Masu Zaben Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a kasar Iran ya bayyana cewa: Matakin da kasar Amurka ta dauka na sake jaddada takunkumin shekaru 10 kan kasar Iran lamari ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, kuma hakan yana kara fayyacewa duniya wace ce Amurka.

A bayanin da shugaban Majalisar Kwararru masu zaben Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iran Ayatullahi Ahmad Jannati ya fitar a yau Talata yana dauke da cewa: Gwamnatin Amurka ta sake fayyace matsayin girman kanta da dabi'arta ta yin kafar ungulu ga dokokin kasa da kasa gami da nuna tsananin kiyayya ga al'ummar Iran, saboda sake tsawaita takunkumin da ta kakaba kan kasar Iran har na tsawon shekaru 10 mai take "ISA" mataki ne na bangare guda da ke matsayin kafar ungulu ga yarjejeniyar da aka cimma kan shirin makamashin nukiliyar Iran.

Ayatullahi Jannati ya kara da cewa: Tuni dama Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Mahukuntan Amurka ba abin dogaro ba ne saboda basu kasa a gwiwa wajen ganin sun cutar da juyin juya halin Musulunci a duk lokacin da dama ta samu gare su.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky