Larijani: Kare Musulunci Yana Daga Cikin Darussan Ashura

  • Lambar Labari†: 784218
  • Taska : Hausa.irib.ir.
Brief

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran yace,Kare Addinin Musulunci Na Daga Cikin Darussan Ashura.

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran da ya ke gabatar da jawabi a jiya juma'a, ya bayyana cewa; Kare addinin musulunci da biyayya ga jagoran addini suna daga cikin darussan da Ashura ke koyarwa.

Dr. Ali Larijani  ya kuma yi managa akan shahidan Iran tare da cewa; sun dauki darussansu ne daga Ashura, abinda su kuma ya maida su zama ginshikin ci gaban da Iran ta samu.

Shugaban Majalisar Shawarar Musluncin ta Iran, ya kara da cewa: Makiyan Jamhuriyar Musulunci Suna da masaniyar cewa; Mutanen Iran suna kaunar iyalan gidan manzon Allah (a.s.w.a) kuma suna biyayya ga jagoran addini da hakan ya ke a matsayin ginshikin tsayin dakarsu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky