Iran Ta Ja Kunnen Amurka Dangane Da Kai Hari Kasar Siriya

  • Lambar Labari†: 783026
  • Taska : Hausa.irib.ir.
Brief

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ja kunnen kasar Amurka dangane da shiga yakin kasar Siriya kai tsaye, tana mai cewa yin hakan yana iya zama tamkar 'kisan kai' ga sojojin Amurkan.

Tsohon ministan harkokin waje kuma babban mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran din kan harkokin waje Dakta Ali Akbar Velayati ne ya bayyana hakan yayin da yake magana kan maganganun wasu jami'an Amurkan na shiga cikin yakin Siriyan kai tsaye inda ya ce ko shakka babu hakan ba zai haifar wa Amurkawan wani da mai ido.

Dakta Velayatin ya kara da cewa, shekaru 6 kenan al'ummar Siriyan suke ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar tsoma bakin 'yan kasashen waje a kasar, don haka a nan gaba ma suna da karfin tinkarar tsoma baki da hare-haren sojojin Amurka da sauransu.

Cikin 'yan kwanakin nan dai ana ta magana dangane da wani sabon shiri da Amurkan take da shi na kai hare-haren soji kai tsaye a kasar Siriya da kuma sojojin kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky