Shugaban Iran Ya Aike Da Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Shugaban Uzbekistan

  • Lambar Labari†: 776561
  • Taska : Hausa.irib.ir.
Brief

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya aike da sakon ta'aziyyar gwamnati da al'ummar Iran ga gwamnati da al'ummar kasar Uzbekistan saboda rasuwar shugaban kasar Islam Karimov wanda ya rasu a jiya Juma'a.

A cikin wata wasika da ya aike wa  mukaddashin shugaban kasar ta Uzbekistan Nigmatilla Yuldashev a jiya Juma'ar shugaba Ruhani ya bayyana alhini da juyayinsa ga iyalan tsohon shugaban, gwamnatin kasar da kuma dukkanin al'ummar kasar Uzbekistan din saboda rasuwar shugaba Islam Karimov.

A jiya Juma'a  ce gwamnatin kasar Uzbekistan din ta sanar da cewar shugaban kasar Islam Karimov ya rasu yana dan shekaru 78 sakamakon bugun zuciya da yayi sanadiyar shanyewar jikinsa. 

A yau Asabar ne ake sa ran za a yi jana'izarsa a garin Samarkand kamar yadda shari'ar Musulunci ta tanada kana kuma a rufe shi a wajen.

Shugaba Islam Karimov dai ya mulki kasar Uzbekistan din na tsawon shekaru 27.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky