Zarif Ya Gudanar Da Tattaunawa Tare Da Shugaban Kasar Ecuador

  • Lambar Labari†: 774387
  • Taska : Hausa.irib.ir.
Brief

A ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran yake gudanarwa a kasashen Latin Amurka,a jiya ya gudanar da tattaunawa tare da shugaban kasar Ecuador Rafael Correa a birnin Quito.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya bayar da rahoton cewa, a yayin ganawar, bangarorin biyu sun tabo batutuwa da suke da alaka da diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, musamman batutuwa na bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma cinikayya a tsakaninsu.

Shugaban kasar ta Ecuador ya bayyana kasar Iran a matsayin babbar kawa gare su a harkokin tattalin arziki da cinikayya, musamman bayan janye takunkumi a kan kasar ta Iran, inda za su ci gaba da aiki a dukkanin bangarorin domin ci gaban kasahensu.

Shi a nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana dangantankatar da tsakanin kasar da Ecuador da cewa, dangantaka ce mai karfi, tare da yaba wa kasashen latin Amurka kan yadda suka kasane a sahun gaba wajen kyautata alakarsu da Iran a lokacin da manyan kasashen duniya suka kakaba mata takunkumi.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky