Kasashen Iran Da Norway Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyoyi Na Bunkasa Tattalin Arziki

  • Lambar Labari†: 772978
  • Taska : Hausa.irib.ir.
Brief

Kasashen Iran da Norway sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi na bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.

A ziyarar aiki da ministan harkokin wajen kasar Norway Borge Brende ke gudanarwa a kasar Iran, a yammacin jiya an sanya hannu tsakanin Iran da kuma kasar ta Norway kan yarjeniyoyi da suka hada da bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya, da kuma hada-hadar kudade ta hanyar bakunan kasashen biyu, kamar yadda kuma suka cimma yarjejeniya kan cinikin danyen man fetur wanda Norway za ta rika saye daga kasar ta Iran.

Ministan harkokin wajen kasar ta Norway ya gana da mayna jami'an gwamnatin kasar Iran, da suka hada da shugaba Hassan Rauhani, gami da takwaransa na kasar ta Iram Muhammad Jawad Zarif, sai kuma shugaban majalisar dokokin kasar Ali Larijani.2888


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky