Dakarun Kare Juyi Na Iran Sun Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda A Kasar

  • Lambar Labari†: 760665
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran sun sami nasarar tarwatsa 'yan wasu kungiyoyin 'yan ta'adda su biyu da suka yi kokarin shigowa kasar daga kasar Iraki inda suka hallaka wani adadi na 'yan ta'addan.

Babban hafsan sojin kasa na dakarun kare juyin Birgediya Janar Muhammad Pakpour ne ya sanar da hakan inda ya ce 'yan ta'addan suna kokarin shigowar kasar Iran din ta yankin Oshnavieh da ke kan iyakar kasar da kasar Iraki don aikata ayyukan ta'addanci inda bayan wani gumurzu mai tsanani a tsakaninsu, dakarun kare juyin suka sami nasarar tarwatsa su da kuma kashe wani adadi na 'yan ta'addan.

Har ila yau a cikin wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin na sansanin Hamza shugaban shahidai (a.s) suka fitar sun bayyana cewar a yayin wannan gumurzun dakarun kare juyin sun sami nasarar hallaka 'yan ta'adda 9 daga cikin 'yan ta'addan da suke kokarin shigo Iran din suna masu sake jaddada aniyarsu na ci gaba da kare kasar Iran din daga duk wata barazanar da za ta iya fuskanta.

A farkon wannan makon ma dai rundunar sojin Iran ta sanar da hallaka wasu 'yan ta'adda goma a wasu hare-haren da suka kaddamar a yankunan arewa maso yamma da kudu maso gabashin kasar ta Iran.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky