Iran: Al'ummar Iran Ba Za Su Je Hajjin Bana Ba, Saboda Kafar Ungulun Saudiyya

  • Lambar Labari†: 757165
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da cewa a wannan shekarar ba za ta tura alhazan kasar zuwa aikin Hajjin bana ba, saboda kafar ungulun da mahukuntan Saudiyya suke ci gaba da yi ga kokarin da gwamnatin ta Iran take yi wajen ganin ta tura alhazan nata.

Ministan al'adu da shiryarwa ta Musulunci ta kasar Iran Ali Jannati ne ya sanar da hakan a yau din nan Lahadi inya ce bisa la'akari da irin mu'amalar da mahukuntan Saudiyya suka yi da tawagar Iran da ta tafi can don tattaunawa kan batun hajjin bugu da kari kan ci gaba da kafar ungulun da suke yi ga dukkanin kokarin da Iran ta yi wajen ganin ta tura alhazan nata, don haka mutanen Iran ba za su je aikin hajji na bana ba.

Ita ma a nata bangaren hukumar alhazan kasar Iran, cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din ta ce duk da kokarin da Iran ta yi wajen tattaunawa da mahukuntan Saudiyyan kan wannan batun, to amma mahukuntan Saudiyyan sun ci gaba da rufe ido kan hakkokin alhazan Iran na sauke faralin don haka ta ce gwamnati ba za ta sanya rayukan 'yan kasarta cikin hatsari ba.

Sau biyu Iran tana tura tawagarta don tattaunawa da mahukuntan Saudiyyan kan batun hajji, amma dai bangarori biyun sun gagara cimma yarjejeniyar da ta za ta tabbatar da tsaron lafiyar maniyyatan Iran.

A yayin Hajjin bara ne dai dubban mahajjata, da suka hada da mahajjatan kasar Iran da dama suka rasa rayukansu biyo bayan turmutsitsin da aka samu a Mina wanda kasar Iran da ma wasu kasashen suka dora alhakin hakan kan mahukuntan Saudiyyan saboda sakacin da suka nuna.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky