Shugaba Buhari Ya Mika Sakon Ta'aziyya Ga Shugaba Iran Rauhani

  • Lambar Labari†: 804815
  • Taska : Pars Today
Brief

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani zuwa ga shugaban kasar Iran Hassan Rauhani.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da shugaba Buhari ya aike wa shugaba Rauhani, ya bayyana cewa hakika an yi babban rashi na mutumin da ke da bababn tasiri ta fuskar siyasa da gagarumin ci gaba da kasar Iran ta samu.

Shugaba Buhari ya ce hakika ayyukan da Rafsanjani ya yi wajen ci gaban kasarsa, za su ci gaba da wanzuwa a kasar Iran, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi na wani babban jigo a dukkanin bangarori na siyasa da zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a kasar ta Iran.

Shugaba Rauhani ya yi godiya ga shugaba Buhari dangane da sakon nasa tare da yin fatan alkhairi ga dukkanin al'ummar Najeriya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2017)
پیام امام خامنه ای به مسلمانان جهان به مناسبت حج 2016
We are All Zakzaky