Jagoran Juyin Muslunci Na Iran Ya Sallahci Jana'izar Tshohon Shugaban Kasar Ayatullahi Rafsanjani

  • Lambar Labari†: 804046
  • Taska : Pars Today
Brief

A Jamhuriya musulinci ta Iran, dubban al'ummar kasar ne sukai tururuwa zuwan babban masallacin Juma'a na kasar dake Tehran babban birnin kasar domin halartar sallar jana'izar tsohon shugaban kasar Akbar Hashemi Rafsandjani wanda Allah yayi wa rasuwa a ranar Lahadi data gabata.

Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ne Ayatullah Ali Khamenei ne ya jagoranci sallar jana'izar mirigayin wace kuma mayan malumma na  kasar da jami'an gwamnati suka halarta.

Za'a dai binne Mirigayin a hubbaren Iman Khomaini dake Tehran babban birnin kasar a yau Talata.

kafin hakan dai an shiga zamen makoki na kwanaki uku domin juyayin rasuwar tsohon shugaban kasar wanda shi ne shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin muslunci ta Iran.

Da yammacin Ranar Lahadi ne Allah ya yiwa Rafsandjani rasuwa sakamakon matsalar zuciya.

A rayuwarsa Rafsanjani ya rike shugabancin kasar Iran daga shekarar 1989 zuwa 1997.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky