An Gwabza Fada Kusa Da Damascus Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

  • Lambar Labari†: 801723
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Hukumar kare hakkin bil adama ta kasa a Syria ta ce an gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da kuma 'yan tawaye masu dauke da makamai a kusa da birnin Damascus a wannan Juma'a.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta da kasashen Rasha da Turkiyya suka cimma wace ta fara aiki a cikin daren jiya Alhamis.

Hukumar ta OSDH ta ce yana da yiwa dai a yanzu a kai ga sanin ko wanne bangare ne ya karya yarjejeniyar a yankin na Wadi Barada dake arewa maso yammacin Damascus babban birnin kasar ta Syria.

A halinda ake ciki dai ko wanne bangare na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yankin Wadi Barada da kuma Ain Al-Fije dake nisan kilomita 15 daga arewa maso yammacin Damascus ya kasance yankin dake samar da ruwan sha ga Birnin, kuma kusan mako guda kenan da babban birnin ke fama da matsalar ruwan sha wanda gwamnatin ke zargin 'yan tawayen da lalatawa.

A cewar MDD kimanin mutane miliyan hudu ne dake birnin Damascus da kewaye ke fama da matsalar ruwan sha tun ranar 22 ga watan Disamban nan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky