Harin Ta'addanci Ya Jikkata Jakadan Rasha A Kasar Turkia

  • Lambar Labari†: 799364
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Rahotannin da suke fitowa daga kasar Turkia a datsu datsu nan sun nuna cewa Jakadan kasar Rasha a birnin Ankara na kasar Turkia ya ji mummunan raunuka bayan an harbe shi da bindiga a yau Litinin.

Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bada labarin cewa an harbi Jakada Andrey Karlov ne a lokacinda yake ziyartar wani bajekolin kayakin aikin hannu a birnin Ankara a yammacin yau Litinin a lokacinda wasu yan bindiga suka bindige shi, inda a halin yanzu yana jinya a wani asbiti a birnin. 

Tashar Television ta NTV ta kasar Turkia da kuma CNN -da harshen turkanci sun bayyana cewa jakadan ya ji mummunan raunuka kuma an ji karin harbe harbe a wurin da aka harbe shi bayan wani lokaci.

A bangaren gwamnatin Rasha dai ta tabbatar da cewa Jakadan kasar a Turkia Andrey Karlov ya rasu sanadiyar harbin da wani dan bingida yayi masa a lokacinda yake jawabi a wani taron aikin hannu a abirnin Ankara, kuma wanada ya kashe shin ya bayyana cewa wannan shi ne sakamakon abinda Rasha ta yi a halab na kasar Siria.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky