Rasha ta aika taimakon Ton 150 zuwa Birnin Halab na Siriya

  • Lambar Labari†: 795938
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Rasha ta aika da taimako na Ton 150 zuwa yankunan da aka 'yanto na Birnin Halab a Kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Edward Govryvof jami'i a Ma'aikatar leken asiri ta Dakarun tsaron Rasha na cewa a yayin da Majalisar Dinkin Duniya gami da kasashen Turai suka kauracewa bayar da taimakon a yankunan da aka ceto daga mamayar kungiyoyin 'yan ta'adda a birnin Allepo, Gwamnatin kasar ta tura taimakon Ton 150 na gayan agaji  zuwa ga yankunan.

Mista Edeward ya ce duk da cewa cibiyar kasar Rasha ita ce ke da alhakin sanya ido a yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Gwamnati da 'yan tawaye kuma ita ce ke daukan nauyin kai taimakon gaggauwa a kasar ta Siriya, a makun da ya gabata ma kimanin Ton 280 ne da suka hada a kayan abinci , da kuma abinda Al'umma ke bukata na gudanar da rayuwa aka aike da su zuwa siriya domin a raba a tsakanin Al'ummar dake rayuwa a yankunan da aka 'yanto na birnin Allepo.

A bangare guda Kakakin Ma'aikatar tsaron Rasha ya nuna takaicinsa kan kin aike da taimako zuwa yankunan da aka tsarkake daga hanun 'yan tawaye na yankin Allepo daga Majalisar Dinkin Duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky