Kasar Iran Tayi Barazanar Mayarwa Da Amurka Martani

  • Lambar Labari†: 795628
  • Taska : VOA
Brief

Kasar Iran tayi barazanar mayar da martini bayan da Majilisar dattijan Amurka ta bada umurnin kara tsawaita takunkunmi ta akan kasar ta Iran, domin ko duka ‘yan Majilisar daga jamiyyun kasar sun amince cewa wajibi ne a tabbatar an tilasta yarjejeniyar nan da aka cimmawa da kasar ta Iran.

Iran dai ta hakikance cewa ta cimma sharuddan da aka cimmawa tsakanin ta sauran kasashen nan da suka yi yarjejeniya da ita akan batun makamashin Nuclear.

Mai Magana da yawun Ministan harkokin wajen na Iran ne Bahram Ghasenni, yace kara waadin takunkumin tamkar keta haddin yarjejeniyar da aka kulla ne.

Sai dai Ghasseni bai bayyana ainihin takaimaiman matakin da za a dauka ba.

A cikin watan da ya gabata ne dai shugaban addinin kasar Ayotollah Ali Khameni yace kara tsawaita takunkumin da Amurka ke cewa zata yi tamkar keta yarjejeniyar da aka cimmawa ne kuma ba zasu yi shiru ba wanda musu cas to zasu ce masa kule.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky