Jami'an Tsaron Iran Sun Hallaka Daya Daga Cikin Shugabannin ISIS A Kan Iyakar Kasar

  • Lambar Labari†: 795024
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya sanar da da cewa jami'an tsaron Iran sun sami nasarar hallaka daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a kan iyakar kasar a kokarin sa na shigowa cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na Iran ya bayyana cewar ministan tsaron cikin gida da tattaron bayanan sirrin na Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana haka ne a wajen wani taro don tunawa da zagayowar ranar rasuwar Ma'aikin Allah (s) da aka gudanar a garin Karaj da ke wajen birnin Tehran inda ya tabbatar da labarin cewa jami'an tsaron na Iran sun sami nasarar hallaka Abu Aisha al-Kurdi, daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar ta Da'esh tare da wasu mukarrabansa a kokarin da suke yi na shigowa cikin Iran.

Ministan ya kara da cewa shi dai wannan dan ta'addan ya so shigowa kasar ta Iran ne tare da wadannan mutane da nufin kai hare-haren ta'addanci birnin Tehran, babban birnin kasar ta Iran, inda jami'an tsaron na Iran suka sami nasarar hallaka shi tare da jama'ar tasa bayan sun sami wasu bayanai na sirri kan kokarin shigowarsu.

Wasu kafafen watsa labaran na Iran sun ce jami'an tsaron sun hallaka Abu Aisha al-Kurdi din a garuruwan da suke kan iyaka na lardin Kermanshah.

Sayyid Alawi ya kara da cewa a lokuta da dama 'yan ta'addan sun so shigowa Iran din sai dai jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kamawa da kuma hallaka wasu da dama daga cikinsu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky