Yau Ne Kasashen Musulmi ke Makokin Wafatin Manzon Allah (s)

  • Lambar Labari†: 794819
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Miliyoyin musulmi a nan Iran da wasu kasashen duniya suna makakin wafatin manzon All... (a) da kuma shahadar Babban Jikansa Imam Hassan Al-Mjtaba (a).

Ranar 28 ga watan safar na ko wace shekara ta hijira kamaria ita ce ranar wafatin manzon Al..(s) da kuma shahadar babban jikansa Imam Hassan almustaba (a). A nan iran dai musulmi masu yawa sukan taro na haramin Imam Rida dake mashad da kuma wasu wurare da ake da haramomi na iyalan gisan manzon Al..(s) a kasar don zaman makoki da kuma juyayi kan wadan nan rashin.

An haifi manzon All..(s) a shekara ta 570 M, ya fara karbin sakon All.. na karshe ga bil'adama wato Alqur'ani yana dan shekara 40 a duniya, sannan ya rashe yana dan shekara 63 a duniya bayan isar da sakon All.. da kuma kafa daular musulunci na tsawon shekaru 23.

Har'ila yau a karshen watan na safar ne za'a gudanar da makokin shahadar Imam Aliyu Bin Musa Al-rida Limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s).288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky