An Tarwatsa Wata Kungiyar 'Yan Ta'adda A Kasar Iran

  • Lambar Labari†: 793730
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Ma'aikatar tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran ta sanar da samun nasarar tarwatsa wata wasu gungun 'yan ta'adda a gabashin kasar da suke da shirin aiwatar da ayyukan ta'addanci a kasar.

Yayin da yake sanar da hakan, mataimakin ministan cikin gidan kasar Iran kan lamurran da suka shafi tsaron Husain Zolfaqari ya bayyana cewar jami'an tsaron ma'aikatar cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran din sun sami nasarar tarwatsa wata kungiya ta 'yan ta'adda da suke kokarin aiwatar da ayyukan ta'addanci a Gabashin kasar ta Iran.

Mr. Zolfaqari ya kara da cewa a yayin harin da aka kai musu, jami'an tsaron sun sami nasarar hallaka daya daga cikin 'yan ta'adddan guda da kuma kama wasu guda uku daga cikinsu., kamar yadda kuma ya ce an samu wasu ababe masu fashewa a tattare da su.

Jami'an tsaron kasar ta Iran dai sun jima suna fada da kuma gumurzu da 'yan kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kokarin kai hare-hare da sauran ayyuka na ta'addanci a cikin kasar musamman a yankunan da suke kan iyakokin kasar ta Iran da wasu kasashe a kokarin da 'yan ta'addan suke yi na shigowa kasar inda a lokuta da dama suke samu nasarar hallakawa da kuma kame 'yan ta'addan bugu da kari kan kwace wani adadi mai yawan gaske na makamai da ababen fashewa.

A makon da ya wuce ma mataimakin ministan cikin gida da tattaro bayanan sirrin na Iran ya sanar da nasarar da jami'an ma'aikatar suka samu na kwace ton biyu da ababe masu fashewa daga wajen 'yan ta'addan kungiyar Da'esh a garin Garamsar, da ke kudu maso gabashin birnin Tehran, babban birnin kasar Iran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky