Iran Ta Yi Watsi Da Zargi "Maras Tushe" Na Wasu Kasashen Larabawa A Kanta

  • Lambar Labari†: 792581
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jakadan Iran kana kuma wakilin kasar na dindindin a Majalisar Dinkin Dinkin Gholam Ali Khoshroo ya yi watsi da zargi 'maras tushe' da wasu kasashen larabawa suka yi na cewa Iran tana tsoma musu baki cikin harkokinsu na cikin gida.

Jakadan na Iran ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan Ban Ki Moon bayan da wasu kasashen larabawan da suka hada da Bahrain, Masar, Jordan, Kuwait, Morocco, Oman, Qatar, Saudiyya, Sudan, UAE da Yemen suka zargi Iran din da abin da suka kira kokarin wargaza musu kasashensu da kuma goyon bayan kungiyoyin 'yan ta'adda, inda ya ce babu kamshin gaskiya cikin wannan zargin.

Jakadan na Iran yayi watsi da wannan zargi na kasashen da ya kira 'kasashen da a baya su ne kan gaba wajen taimakon tsohon mulkin kama-karya na Iraki Saddam Husain da makamai da kudaden don ya yaki Iran tsawon shekaru takwas na kallafaffen yaki.

Mr. Khoshroo ya kara da cewa: Abin ban dariya ne a ce gwamnatocin da su kansu su ne suke karfafa tsaurin ra'ayi da akidar takfiriyya a Iraki da Siriya da sauran kasashe amma suna zargin Iran da taimakon ta'addanci.

Sakamakon ci gaba da shan kashin da wasu kasashen larabawa irin su Saudiyya suke yi a Iraki da Siriya hakan ne ya sanya su komawa suna zargin Iran da tsoma baki cikin lamurran kasashen larabawa don rufe irin goyon bayan  ta'addancin da suke yi a wadannan kasashe.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky