Jagora Imam Khamenei: Sakamakon Zaben Amurka, Ba Shi Da Wani Bambanci A Wajenmu

  • Lambar Labari†: 792361
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Iran dai ba ta cikin wata damuwa dangane da sakamakon zaben kasar Amurka, to sai dai tana cikin shirin fuskantar koma mai zai faru, yana mai cewa sakamakon zaben ba shi da wani bambanci a wajen Iran.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne  a wata ganawa da yayi da dubun dubatan mutanen garin Esfahan inda ya ce sabanin wasu a duniya da ko dai suke cikin damuwa ko kuma farin cikin sakamakon zaben Amurkan, mu dai ba ma bakin ciki kuma ba ma farin ciki, don kuwa sakamakon zaben ba shi da wani bambanci a wajenmu.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ba mu da wata damuwa, sannan kuma cikin yardar Allah muna cikin shirin fuskantar duk wani abin da zai iya biyo ba.

A wani bangare na jawabin na sa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewar al'ummar Iran ta hanyar tsayin daka da kuma riko da koyarwar Musulunci da juyin juya halin Musulunci za su sami nasarar magance matsalolin da suke fuskanta.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky